✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsawa ta hallaka shanu 36 a Ondo

Wani makiyayi mai suna Ladan a karshen makon nan ya ce, ya rasa shanu 36 sakamakon saukar wata tsawa a kusa da inda yake kiwo…

Wani makiyayi mai suna Ladan a karshen makon nan ya ce, ya rasa shanu 36 sakamakon saukar wata tsawa a kusa da inda yake kiwo a garin Ijare yankin Idanre karamar Hukumar Ifedore a jihar Ondo.

Ladan, dai dan asalin jihar Kwara ne, amma ya kai ziyara jihar Ondo tare da dabbobinsa a lokacin da suke kiwo tsawar ta sauka wanda ta haddasa mutuwar shanun.

Shugaban Kungiyar Miyetti Allah na jihar, Alhaji Bello Garuba ne ya tabbatarwa Wakilin mu abin da ya faru game da mutuwar shanun, inda ya bayyana rashin jin dadinsa akan abin da ya faru.

Alhaji Bello, ya kara da cewa, ba su da wani abun yi Allah ne ya kaddara faruwar hakan, kuma ya bukaci wanda ya mallaki shanun da ya dauki kaddara ya yi hakuri.