✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsaron Katsina: Za mu dora daga inda Masari ya tsaya —APC

Jam’iyyar APC mai mulkin Jihar Katsina ta yi alkawarin dorawa daga inda ta tsaya a fannin tsaro idan ta ci zaben gwamnan jihar da ke…

Jam’iyyar APC mai mulkin Jihar Katsina ta yi alkawarin dorawa daga inda ta tsaya a fannin tsaro idan ta ci zaben gwamnan jihar da ke tafe.

Dan takarar gwamnan jihar a Jami’ar APC, Dikko Dikko Umar Radda, ne ya yi alkawarin a taron a Zauren Al’Umma na Katsina wanda kamfanin Media Trust tare da hadin gwiwar Cibiyar Cigaban Dimokuradiyya  (CDD) da wasu kafafen yada labarai suka shirya.

Dikko Radda, wanda abokin takararsa, Faouq Lawal Jobe, ya wakilta ya bayyana cewa su biyun suna da kwarewa, kasancewarsu malaman makaranta, ma’aikatan banki kuma wadanda suka taka rawa a gwamnatin mai ci daga shekarar 2015.

Ya ce zasu zasu maida hankali wajen inganta tsaro, ilmi da kuma kiwon lafiya da sauran fannonin rayuwa.