✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsaro: Buhari ya manta da rantsuwarsa da Al-Qur’ani — ACF

Buhari yana da sanin hukuncin rantsuwa da Al-Qur’ani ba tare da girmama rantsuwar ba.

Kungiyar Dattawan Arewa (ACF) ta ce matsalar rashin tsaro ta ci gaba da tabarbarewa musamman a Arewacin Najeriya tun bayan ganawar da ta yi da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a watan Oktoba inda ta ba shi shawara da ya mayar da hankali kan tabbatar da aminci a yankin.

Cikin wata sanarwa da Kungiyar ta fitar mai dauke da sa hannun Jami’inta na Hulda da Al’umma, Emmanuel Yawe, ta kirayi Shugaba Buhari da ya ji tsoron Allah kuma ya girmama rantsuwar da ya yi da Al-Qur’ani ta kare martabar al’ummar kasar nan.

A cewar kungiyar, “Babu bukatar mu ci gaba da kiran Shugaba Buhari a kan ya girmama rantsuwar da ya yi, domin kuwa ya fi kowa sanin duk wani hukunci na Allah Madaukaki da suka shafi yin rantsuwa da Al-Qur’ani ba tare da girmama rantsuwar ba.”

ACF ta ce tana cikin zulumi da damuwa matuka dangane da yadda ’yan bindiga ke zubar da jinin al’umma a Arewacin kasar wanda a cewarta hakan na faruwa ne duk da shaci fadin da Ministan Harkokin ’Yan Sanda ya yi na cewa an dakile ta’addancin ’yan bindiga a kasar.

Kungiyar ta yi Allah wadai da yadda satar mutane da kuma kashe su ke kara ta’azzara a cikin wannan lokaci musamman a jihohin Arewa maso Tsakiya da maso Yammacin kasar.

Ta bayyana damuwa kan yadda a baya-bayan nan ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane ke cin karensu babu babbaka a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, inda ta buga misali da yadda aka yi  garkuwa da wasu dalibai 9 na jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya.

Kazalika kungiyar ta yi tir da yadda wasu manyan jami’an ’yan sanda 12 suka fada komar masu garkuwa da mutane a kan hanyar Zamfara zuwa Kaduna, inda ta ce duk wannan na faruwa ne bayan kanzon kuregen da Ministan Harkokin ’Yan Sanda ya yi na cewa an gurgunta masu ta’addanci a yankin Arewa.