✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsarin tekunan duniya da abubuwan da ke cikinsu (6)

Binciken KimiyyaGano Tekun Atlantika a duniya ya zaburar da hukumomi da kasashe da ma wasu cibiyoyin binciken kimiyya musamman na teku, gudanar da bincike don…

Binciken Kimiyya
Gano Tekun Atlantika a duniya ya zaburar da hukumomi da kasashe da ma wasu cibiyoyin binciken kimiyya musamman na teku, gudanar da bincike don tantance abubuwa da yanayin wannan mahalli.  Babban binciken kimiyyar teku na farko da aka fara gabatarwa a wannan teku na Atlantika shi ne wanda  Ingila ta gudanar tsakanin shekarar 1872 zuwa 1876; tsawon shekaru hudu kenan.  Ta gudanar da wannan bincike ne a kan wani babban jirgin ruwa irin na wancan zamani mai suna: “HMS Challenger.”  Daga nan kuma aka sanya wa wannan shirin bincike suna: “The Challenger.”  Wannan bincike na kimiyya ya fara ne ya kuma kare duk a cikin Tekun Atlantika.
Daga shekarar 1925 zuwa 1927 sai  Jamus ita ma ta leko cikin tekun.  Bincikenta ya ta’allaka ne ga bangaren Kudancin tekun na atlantika, na tsawon shekaru biyu.  Wannan shirin bincike ta sa masa suna: “German Meteor Edpedition.”  Bulaguro ne na binciken kimiyya da ya shafi bangaren Kudancin tekun kadai.  Cikin shekarar 1949 kuma sai Jami’ar Kolombiya da ke Amurka ta shirya nata binciken kan wannan teku.  Wannan bincike an gudanar da shi ne karkashin wata cibiyar binciken kimiyya da ke jami’ar mai suna:  “Lamont-Doherty Earth Obserbatory.”  Cibiya ce dake gudanar da bincike kan dukkan abin da ya shafi kasa, da teku da abubuwan da ke kansu na halittar Ubangiji.
Bincike na karshe shahararre da za mu dakata a kan shi shi ne wanda hukumar Lura da Tekuna da Yanayi na Amurka ta gudanar.  Wannan hukuma ita ce: “United States Hydrographic Office.”  Ita ma ta gudanar da bincike na musamman kan Tekun Atlantika.
Shahararrun Balaguro
Tekun Atlantika teku ne da ya dara sauran tekuna samun masu balaguro a cikinsa; ko dai na kasuwanci, ko bincike, ko yawon bude ido, ko na kuru, ko kuma don ganin ido. Farin wata ne, sha-kallo.  Wannan ba abin mamaki ba ne idan muka yi la’akari da bigiren da yake.  Teku ne da ya hade manyan nahiyoyin duniya uku musamman; ya hade nahiyar Turai da Amurka, domin a tsakaninsu yake kai tsaye.  Ya hade nahiyar Asiya da Afirka da Latin Amurka, ta bangaren Kudanci kenan.  Domin daga Kudancin Amurka kana iya shigowa Yammacin Afirka, daga nan kuma ka dire a Tekun Indiya ko Tekun Maliya, kamar yadda muke ambatonsa, wanda kai tsaye zai sadar da kai da nahiyar Asiya da gabashin duniya.  Idan ka koma makurar arewacin turai ma haka lamarin yake.  Tekun Atlantika ya hade da Tekun Aktik.
Wannan dalili ya sa aka samu masu bulaguro da dama, musamman tun a zamanin baya har zuwa wannan lokaci da muke ciki.  A tsakanin shekara ta 600 – 400 kafin zuwan Annabi Isa (amincin Allah Ya kara tabbata a gare shi), tarihi ya nuna babban mai bulaguron teku a wancan lokaci mai suna: “Hanno the Nabigator” ya kutsa cikin Tekun Atlantika, inda ya dangana zuwa Yammacin Afirka, daga can kuma ya nausa zuwa daidai bigiren Kambun duniya (Ekuator).  Hanno dai shahararren mai balaguron teku ne a wancan zamani.
Daga shekarar 980 zuwa 982 bayan daukaka Annabi Isa (AS) kuma, mai bulaguro Enrik, wanda aka fi sani da lakabin: “Enrik the Red,” shi ma ya ketara Tekun Atlantika.  Shi ne wanda ya gano tsibirin Greenland, tare da wani bangaren Kudanci da Arewacin Amurka (South and North America).  Ana shiga shekara ta 1000 kuma sai dansa mai suna Leif Ericson ya gaji sana’ar mahaifinsa, inda ya zama mutum na farko da ya fara taka  gabar gabashin Kanada a yau.  Da Enrik da dansa Leif dai, dukkansu ‘yan asalin Norway ne, duk da cewa sun bar kasar, inda suka ci gaba da zama a duk kasar da suka bude ko suka kafa, har mutuwarsu.
Masu balaguron teku na  Portugal ma sun keta Tekun Atlantika daga shekarar 1419 zuwa 1427, kuma su ne farkon wadanda suka gano kasar Madeira da Azores da ke Meziko a yau.  Kafin wannan bulaguro dai har wa yau, tarihi ya sake nuna mana cewa wata bataliya ta masu balaguro daga  Portugal din dai har wa yau, ta taso a shekarar 1415, inda suka nausa cikin Tekun Atlantika suka doshi  bigiren Yammacin Afirka, daga can suka tsallaka kambun duniya, suka tike a Tekun Indiya (Tekun Maliya).  Ba su karasa tekun maliya ba sai cikin shekarar 1488.
Shekaru hudu bayan wannan bulaguro nasu, cikin shekarar 1492 sai Christopher Columbus ya yi nasa balaguron, inda ya tsallaka Tekun Atlantika daga Daular Spain da ke gabashi, zuwa yammaci, har a karshe ya dire a wani bigiren Amurka da a yanzu ake kira da suna: “Bahamas.”  Christopher Columbus dai shi ne wanda ya gano kasar Amurka ta yau, cikin wannan balaguro da ya yi a shekarar 1492.  A wancan lokaci ya sa mata suna: “New World,” kuma duk da cewa dan kasar Italiya ne shi, Sarauniyar Spain ce ta dauki nauyin wannan tafiya tasa.  Bayan wannan balaguro ma, ya sake yin wasu zubi uku a lokaci daban-daban.
Bayan balaguron Tekun Atlantika da ya haddasa gano kasar Amurka ta yau a wancan lokaci, cikin shekarar 1496, John Cabot, wani matafiyi shi ma ya keta ruwa cikin bulaguro zubi uku; daga birnin Bristol zuwa Arewacin Amurka.  Shekaru biyu bayan nasa bulaguron, sai Pedro Albares Cabral ya kutsa Tekun Atlantika shi ma, inda tafiyarsa ta tike da shi a kasar Burazil ta yau. Wannan ya faru ne a shekarar 1500.  A cikin shekarar 1519 kuma sai matafiyi  mai balaguro Ferdinand Magellan ya ketara Tekun Atlantika daga Daular Spain da ke gabashin tekun, ya nausa Kudancinsa, har a karshe ya dangana da babban tekun duniya, wato: Pacific Ocean.