Sabon tsarin da kasar Saudiyya ta fito da shi na tantance masu son shiga kasar yana wahalar da masu zuwa kasar.
Aminiya ta gano cewa tsarin da aka fitar a karshen bara yana bukatar duk wanda ke son shiga kasar daga kowace kasa ta duniya sai ya nuna fasfon din kasarsa, sannan ya ba da hotonsa, sannan ya cika fom guda biyu da kuma wadanda za su je aikatau da tukin mota su san dokar kasar. Haka kuma sabon salon shi ne, sai an dauki hoto a na’ura mai kwakwalwa da zai nuna fuska, yatsu da kuma tafukan hannu.
Bincikin Aminiya ya gano cewa an ba wani kamfanin Indiya mai suna bFS Tasheel International kwangilar yin wannan aikin kuma a wurare uku ne kacal ake tantancewa a dukan fadin kasar nan. Wuraren sun hada da Kano da Abuja da Legas. Sannan mutanen Jamhuriyyar Benin, sai sun ziyarci ofishin da ke Legas don a yi masu wannan sabon tsari da ake kira da “biometric.”
Wata mata daga Maiduguri a Jihar Borno ta ce ta kwashe wata uku tana neman a tantance ta amma har yanzu ba a zo kanta ba.
Mataimakin Shugaban kungiyar Masu Shirya Tafiye-Tafiye ta kasa da ke Abuja, Alhaji Tijjani Uba Waru ya ce: “Mun sanar da mahukunta Ofishin Jakadancin Saudiyya halin kuncin da ake ciki, amma sun ce doka ce daga kasarsu. Mun nuna musu cewa abin na haifar da matsaloli domin masu tantacewa uku ne a kan na’urar kwamfuta. Muna neman a ba mu damar tantancewar daga ofisoshinmu tunda a kwamfuta ce, domin kasar Saudiyya ta ba da kuraren lokaci kafin a fahimci abin, ga matsalar yanar gizo da sauransu.”
Ya ce ya dace Ma’aikatar Harkokin kasashen waje da Hukumar Hajji ta kasa da takwaraorinta na jihohi su yi tanadin ganin ba a wahalar da maniyyata Aikin Hajji da Umara da suke kaiwa mutum dubu 95 ba.
Mahukuntar bFS Tasheel sun ki yin bayanin dalilan da suka janwo tafiyar hawainiyar sabon tsarin, sun ce ba su da damar yin magana da manema labarai.
Gwamnatin Tarayya, ta bakin Minista a Ma’aikatar Harkokin kasashen Waje, Hajiya Khadija Bukar Abba Ibrahim, ta ce yayin da ta tarbi Kwamitin Majalisar Wakilai mai kula da al’amuran Najeriya da Saudiyya da batun Aikin Hajji a ofishinta, ta ce ana ta kokarin shawo kan matsalar da kuma tsame maniyyata Aikin Hjaji daga cikin wannan tsari.