Sarauta na nufin shugabancin jama’a bisa tsarin mulki na addini ko na al’ada ko shugabancin sana’ar da mutum ya rayu a cikinta ko ya gada.
Sarauta ta kasu kashi-kashi. Kamar yadda aka fada da farko, akwai sarauta ta mulkin kasa wacce ake ba mutum a matsayinsa na sarkin gari, kamar misalin Zazzau wanda shi ne Sarkin kasar Zazzau baki daya. Haka kuma akwai sarkin musulmi wanda yake rike da mukamai biyu na sarauta, ga shi shi ne sarkin Sakkwato kuma shi ne sarkin musulmi kuma shugaban sarakunan musulmi. Bugu da kari, akwai sarauta ta sana’a wadda a sakamakon sana’ar da kake yi ake ba ka wannan sarauta don ka yi mulki ko shugabanci irin masu wannan sana’a taka. Misali, sarkin Noma ko sarkin Kasuwa ko sarkin dawa. Wadannan masu sarautu suna da irin tasu daukaka da mahimmanci wurin mutanen da suke shugabanta don kare darajar sana’arsu, wasu kuma sarautu ana bayar da su ne bisa gado, kamar sarautar kira da wanzanci wadanda ake nada musu sarkin Makera da sarkin Aska.
Akwai sarauta ta hakimci da sarki ke nada wanda ya cancanta don ya zama wakilin Sarki a wata Gunduma ko wani Gari, kuma yana da masarautarsa da gwargwadon ikon da aka ba shi a wannan yankin da sarki ya tura shi a matsayin Hakimi, Iyan zazzau Hakimin Sabon Garin zariya da ciroman Zazzau Hakimin Likoro. Wadannan duk hakimai ne masu rike da kasa kuma da rawanin sarauta a kansu.
Bayan wadannan hakimai kuma masu sarauta akwai dagatai masu rike da sarauta ta gargajiya, a garuruwan hakimai. Wadannan sarakuna mafi yawanci masu sarautar gadon gado a garuruwansu a kasar zazzau. Ana yi masu lakabi da sarakunan Karkara da Gorori. Irin wadannan sun hada da Sarkin Makarfi, Dagacen Makarfi da sarkin Rubuci, Dagacin Rubuci da Sarkin kaya, Dagacen kaya da Sarkin Marmara, Dagacen Marmarda, Sarkin Furana da Dagacen Furana. Wadannan su ne suke a karkashin hakimi kuma suna da yankin mulkinsu da irin gwargwadon ikon da aka ba su a hannunsu bisa tsari na sarautar.
Banda wannan tsari na dagatai ko magadai akwai kuma masu Unguwanni wadanda suke karkashin Dagatai kuma su ne wakilin Dagatai a Unguwanni a ko’ina a cikin tsarin Sarauta ko a Birni ko a kauye. Ma’ana, a garin cikin tsarin sarauta ko a birini ko ko a kauye. Ma’ana, a garin sarki ko Hakimi ko Dagace ko’ina akwai masu Unguwanni.
Akwai sarautu irin na addini wanda malamai kawai ake ba wadannan sarautu, kamar Na’ibin Zazzau da Sarkin Ladanan Zazzau da Limamin konan Zazzau da Sarkin Sharifan Zazzau da Mutawallen Zazzau. Wadannan sarautu ne da ake ba malamai, bisa cancanta da irin gogewa ko wurin ilimin addini.
Daga shafin kasar Zazzau a jiya da yau