✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsarin iyali

Wani mutum ne ya je gidan gona ya sayo kwan kaji, ya kawo wa matarsa cewa ta soya masu. Ta shiga kicin ta fara fasa…

Wani mutum ne ya je gidan gona ya sayo kwan kaji, ya kawo wa matarsa cewa ta soya masu. Ta shiga kicin ta fara fasa kwayayen amma kowanne ta fasa sai ta ga babu ruwan kwan a ciki. Da mijinta ya dawo ta gaya masa sai ya yi mamaki, ya dauki kwafsan kwayayen ya koma gidan gona ya shaida wa manajan abin da ya faru. Manaja ya yi mamaki, ya shiga dakin kaji yana cewa: “Aikin wofi, kowane kwai kuma ya zama ba komai ciki!” Sai ya ji kaji sun amsa masa suna cewa: “Maigida, ai mun gano sirrin abin, mu ma Family Planning (tsarin iyali) muka fara.”