✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsarin harajin Najeriya na buƙatar gyara – Gwamnatin Tarayya 

Ministan Yaɗa Labarai da Al'adu, Mohammed Idris, ya yi kira da a sake duba tsarin harajin Najeriya, wanda ya ce yana cike da matsaloli.

Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu, Mohammed Idris, ya yi kira da a sake duba tsarin harajin Najeriya, wanda ya ce yana cike da matsaloli.

Ya jaddada muhimmancin tattaunawa wajen magance taƙaddamar da ke tattare da sabbin ƙudirorin gyaran haraji.

Da yake magana a taron tattaunawa kan ƙudirorin gyaran haraji da aka shirya a Kaduna, Idris ya ce, “A tsarin dimokuraɗiyya, tattaunawa mai ma’ana tana da muhimmanci wajen ci gaban al’umma.

“Dole ne mu bai wa ra’ayoyin mutane daban-daban dama, kuma mu girmama waɗanda ba mu da bambanci da su. Gwamnatin Tinubu ba za ta taɓa keta ƙa’idojin dimokuraɗiyya ba.”

Idris, ya yaba wa Kwamitin Shugaban Kasa kan Gyaran Kuɗaɗe da Haraji kan yadda suka shiga tsakanin al’umma game da sabbin ƙudirorin.

Ya ƙara da cewa, “Shugaba Tinubu ya bayyana a fili cewa za a saurari duk masu ruwa da tsaki tare da tabbatar da an magance dukkanin ƙorafe-ƙorafe.”

Taron, wanda Ƙungiyar Dabarun Sadarwa ta Najeriya (NIPR), ta shirya, ya tara masu ruwa da tsaki don tattaunawa kan muhimmancin gyaran haraji ga ci gaban ƙasa.

Fitattun mutane, ciki har da Sanata Shehu Sani da Sheikh Abubakar Gumi, sun nuna goyon bayansu ga gyaran, inda suka ce hakan zai iya taimakawa wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasar nan.