✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsarin babban manhajar kwamfuta (3)

Muhimman Ayyukan Babbar ManhajaA baya masu karatu sun ji bayanai kan nau’ukan babbar manhaja guda biyu muhimmai da ake da su a duniya, da irin…

Muhimman Ayyukan Babbar Manhaja
A baya masu karatu sun ji bayanai kan nau’ukan babbar manhaja guda biyu muhimmai da ake da su a duniya, da irin siffofin kowacce daga cikinsu.  Wannan zai taimaka wa mai karatu gane kowacce daga cikinsu a duk sadda ya ci karo da kwamfuta, ko ma ya samu nasa. Bayan haka, siffofin da na zayyana ya kebance wadda ke dauke da siffofin ne.  A daya bangaren kuma, kowace babbar manhajar kwamfuta na aiwatar da muhimman ayyuka guda hudu ne, a talakance.  Ma’ana, duk lalacewar babbar manhajar kwamfuta, dole ne a same ta tana iya aiwatar da wasu ayyuka guda hudu da bayaninsu zai zo nan kadan. Rashin iya gudanar da daya daga cikinsu kadai na nuna ba ta cika ka’idar zama babbar manhajar kwamfuta ba ne ko kadan.  Don haka sai mu kiyaye, mu natsu don fahimtar wadannan muhimman ayyuka.  Idan ka saba amfani da kwamfuta ko da na tsawon wata guda ne, ya kamata ka iya tantance wadannan ayyuka nata.  Wadannan bayanai za su zo ne a fayyace.  Allah Ya yi mana jagora, amin.
Alaka da Gangar-jikin Kwamfuta
Babban aiki muhimmi na farko da kowace babbar manhajar kwamfuta ke gudanarwa shi ne hada alaka tsakaninta da gangar-jikin kwamfutar, ko kace kwarangwal; wato Hardware kenan.  Fahimtar hakan ba abu ba ne mai wahala, amma akwai sarkakiya a cikinsa.  Tabbas abu ne sananne cewa daya daga cikin ayyukan ruhin dan adam shi ne hada alaka tsakaninta da gangar-jiki baki daya.  A bangaren babbar manhajar kwamfuta na yin hakan ne ta hanyoyi kamar haka:
Hanyar farko ita ce ta hanyar wasu kananan masarrafai da kowace na’urar sadarwa ke zuwa da ita, wadanda ke ba su damar musayar bayanai tsakaninsu da kwamfuta.  Wadannan kananan masarrafai su ake kira “Debice Dribers” a harshen Turanci.  Duk wata na’urar sadarwa ta zamani – irin su wayar salula, da ma’adanar filash, da babbar ma’adanar kwamfuta, da talabijin kwamfuta da sauransu – duk suna zuwa ne da wadannan kananan masarrafai.  Da zarar ka makala su a jikin kwamfutarka, nan take za ka ga ta ce maka: “Installing Debice Dribers.”  Idan babbar manhaja ta gama loda wadannan masarrafai, sai ta sanar da kai.  Daga nan sai ka ci gaba da amfani da na’urar.  Babbar manhaja takan yi wannan aiki ne a karon farko idan ka loda mata kowace irin nau’urar sadarwa don musayar bayanai ko kallon wasu abubuwa.  Manufar yin hakan shi ne don ta samu cikakken bayani kan suna da nau’in wannan na’urar da aka shigar mata.
Bayan haka, ba wai abubuwan da ake iya makala wa kwamfuta kadai ba, hatta wasu masarrafai ko manhajoji da muke amfani da su a kwamfuta, duk suna da ire-iren wadannan masarrafai masu suna “Dribers” ko “Jami’ai” kamar yadda nake ambatonsu.  Haka a duk sadda kwamfutarka ta kasa kamo tashar Intanet bayan ka sa mata Modem a misali, ko ta ka sa fitar da sauti bayan ka yi kokarin kadawa, ko ta daina nuna hoton bidiyo, alhali kana da masarrafar da ke iya nuna bidiyon lafiyar kalau, to za ka samu matsalar duk ta rashin wadannan “Jami’ai” ne, wato Dribers.  Idan kana son gano haka, ka je “Start”, sai ka hau kan “Computer” ka matsa bangaren daman beran kwamfutarka, wato “Right-Click” sai ka je “Properties” can karshe kenan; ka matsa. Idan shafi ya budo, sai ka lalubo “Debice Manager” daga can bangaren hagu a sama, ka matsa.  
Shi “Debice Manager” wani bangare ne mai matukar muhimmanci, wanda ke dauke da dukkan kananan manhajojin kwarangwal din kwamfutar baki daya, da duk wani abin da ke iya hada alaka tsakanin kwamfutar da wata kwamfutar.  Za ka ga jerinsu tare da sunan kowannen, daga sama zuwa kasa.  Duk inda ka ga tambarin alamar tambaya (kuestion mark) mai launin rawaya, to, na’urar da ke dauke da wannan tambari ta samu matsala kenan.  Ma’ana, babu “Driber” dinta kenan, ko kuma akwai amma ya samu matsala sanadiyyar wata manhaja da ka saukar, wacce ba ta dace da babbar manhajar kwamfutar ba. Wannan ke nuna mana cewa, babbar manhajar kwamfuta ce ke hada alaka tsakanin manhajojin da ke dauke a kanta, da kwarangwal din kwamfutar baki daya.  Ba wannan ba kadai, ita ce ke hada alaka ta hanyar sadarwa, tsakanin mai mu’amala da ita, da ainihin kwarangwal din kwamfutar, kamar yadda bayani ya gabata makonnin baya.
Hanya ta biyu na samuwa ne ta tsarin “Plug and Play” ko “PnP” a gajarce.  Wannan shi ne tsarin da ke tabbatar da alaka tsakanin kwamfuta da duk wani abin da aka makala mata na sadarwa – musayar bayanai wajen shigarwa ko karba.  Tsarin “PnP” wani ginannen tsari ne da kamfanin Microsoft ya fara gina shi tun a babbar manhajarsa mai suna “Windows 95,” babbar manhajarsa ta farko da ta fara yin fice, kafin nau’in Windows dP ta maye gurbinta.  Tun sannan kamfanin Microsoft ke dada inganta wannan tsari, don taimaka wa masu mu’amala da kwamfutar da ke dauke da Babbar manhajar Windows iya mu’amala da bayanan da suke son shigar wa kwamfutar, kai tsaye.  Yadda tsarin yake shi ne, da zarar ka soka ma’adanar filash (Flash Dribe) a jikin kwamfutarka misali, nan take babbar manhaja za ta tsara (Configure) wannan ma’adana, sannan tana iya budo maka abin da ke dauke cikinta (Autoplay) na bayanai nan take (kana iya hana ta yin hakan a bangaren “Control Panel” don kare ta daga kwayoyin cutar kwamfuta masu shigar da kansu nan take da zarar babbar manhaja ta karbi ma’adanar da aka shigar mata). Wannan tsari na “Plug and Play” na da alaka ne na kai tsaye da babbar titin sadarwa da ke jikin kundun kwamfuta, wato “Computer Bus.”