✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsare Tukur Mamu ta’addanci ne —Gumi

DSS dai ta yi ikrarin cewa akwai karin tambayoyi da Tukur Mamun zai amsa.

Fitaccen malamin nan na addinin Islama da ke Jihar Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, ya ce ko dai Hukumar Tsaro ta DSS ta saki Tukur Mamu ko kuma ta gurfanar da shi a gaban kuliya.

Sheikh Gumi wanda ya yi wannan furuci a karatunsa na mako-mako da ya saba gabatarwa a Masallacin Sultan Bello da ke Kaduna, ya ce an cafke Mamu ne saboda rawar da yake takawa ta shiga tsakani wajen sakin wadanda ’yan bindiga suka yi garkuwa da su.

A cewarsa, doka ta tanadi cewa ana gurfanar da duk wanda ake zargi a gaban kuliya bayan sa’a 24 da kama shi.

“Allah Yana jarabtar muminai, kuma wannan wata hanya ce ta jarrabawa daga Allah a kan Mamu.

“Ku kai shi kotu ya fuskanci shari’a don tsare shi a gidan yari ba tare da an bayyana laifinsa ba abun damuwa ne kwarai da gaske.

“Wannan lamari akwai firgici a cikinsa kuma ta’addanci ne. Kama mutane bisa zalunci, shi ma ta’addanci ne; kamar yadda ’yan ta’addan ke yi ta hanyar zuwa gidan mutane su sace su kuma su yi garkuwa da su.

“Ta ya za a yi mu ci gaba da rayuwa a irin wannan yanayi a karkashin gwamnatin da wa’adinta ya zo karshe?

“Babban fatanmu shi ne gwamnatin ta gama lafiya.

“Kuma ba wai don Tukur Mamu aka kama ba, kun san cewa duk wanda aka kama bisa zalunci sai na fito na yi magana, ballantana kuma a kama wanda na sani.

“Ina mai shawartar gwamnatin da ta gaggauta sakinsa kuma ta nemi yafiyarsa komai ya zama tarihi,” a cewar Sheikh Gumi.

Aminiya ta ruwaito cewa, a makon jiya ne jami’an DSS suka kama Tukur Mamu, wanda yake shiga tsakanin gwamnati da ‘yan bindigar da suka yi garkuwa da fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.

A ranar Talata ce jami’an tsaron kasa da kasa na Interpol suka kama tare da tsare Tukur Mamu a filin jiragen sama na birnin Alkahira, a lokacin da ya ke jiran shiga jirgin da zai tashi zuwa Saudiyya.

Sai dai Interpol ta mayar da shi Najeriya bayan tambayoyin da aka yi masa ba tare da samunsa da wani laifi ba, inda saukarsa ke da wuya ‘yan sandan farin kaya na DSS suka cafke shi a Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano.

DSS dai ta yi ikrarin cewa akwai karin tambayoyi da Tukur Mamun zai amsa dangane da matsalolin tsaro da suka addabi kasar.