✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsananin zafi da karancin ruwa ya fara gigita Indiyawa

Masana dai na alakanta matsalar da sauyin yanayi

Idan akwai wata matsala da ke ci wa wasu sassan Kasar Indiya tuwo a kwarya a wannan lokaci, ba ta wuce ta fama da karancin ruwa da kuma matsanancin zafin yanayi ba.

Yankin Rajasthan na Indiya na daga cikin wuraren da ke fama da wannan matsala ta karancin ruwa da kuma matsanancin zafin yanayi kamar yadda rahotanni daga yankin suka tabbatar.

Bayanai sun nuna sakamakon matsanancin zafi da kuma karancin ruwan da yankin ke fama da su, an dauki matakin samar wa al’ummar yankin ruwan sha ta hanyar amfani da jirgin kasa.

An ce kowace rana al’ummar yankin, musamman yara da mata, kan yi cincirundo a bakin layin dogo dauke da bokitai da jarkoki da tukwanen karfe suna jiran zuwan jirgin kasa mai tarago 40 ya kawo musu ruwa kamar yadda ya saba.

Masana sun ce duk da dai yankin kan yi fama da zafin yanayin da kan dara mataki 45 kan ma’aunin celsius, amma wannan karon lamarin ya munana tare da jefa rayuwar mutum biliyan 1.3 cikin mawuyacin hali a fadin Indiya.

Haka nan, sun ce iftila’in na da nasaba da canjin yanayin da ake magana.

Gidan talabijin na Aljazeera ya rawaito wani mazaunin yankin Pali na cewa, “Haka muke fama da matsanancin zafi a yankinmu, kuma ga fama da wahalar ruwa” a daidai lokacin da yake jiran jirgin kasan da ya saba kawo musu dauki.

Jirgin kasan da ke dakon ruwa

Rahotanni sun nuna ruwa lita miliyan biyu jirgin ke dako kowace shiga zuwa yankin don rage wa al’ummar radadin matsalar zafi da karancin ruwan da suke fama da ita.

Al’ummar yankin sun koka kan yadda galibi yaransu kan rasa zuwa makaranta saboda yawon neman ruwa.

Idan dai za a iya tunawa, a 2019 Firaminista Narendra Modi ya kaddamar da wani shirin samar da wadataccen ruwan sha ga talakawan Indiya inda ya sha alwashin samar da ruwan famfo a kowane gida a daukacin kauyukan kasar ya zuwa 2024, amma da alama hakar shirin bai cim ma ruwa ba.