Harkar lafiya a kasar Afghanistan wacce ta dogara kacokam kan tallafin kasashen duniya kusan shekara 20, ta dada tabarbarewa tun bayan karbar mulkin Taliban.
Yanzu haka dai rahotanni sun ce jarirai da kananan yara sun fara fuskantar matsananciyar yunwa bayan da kasashe suka dakatar da bayar da tallafi.
- Mako 2 bayan ziyara a Abuja, Shugaban Afirka ta Kudu ya kamu da COVID-19
- Ba a Najeriya ne kawai ake fuskantar kashe-kashe ba – Fadar Shugaban Kasa
Kasar Amurka dai ta dakatar da tallafin Dala biliyan 9.5, haka ma Asusun ba da Lamuni na Duniya (IMF).
Yanzu haka dai sassa uku na asibitin gwamnati na Indira Ghandi da ke birnin Kabul sun cika makil da mutanen da ke tsananin bukatar taimako saboda rashin lafiya.
Saboda karancin gadajen kwantar da marasa lafiya, akan hada akalla yara biyu zuwa uku a kan gado daya, yayin da iyaye ke shayar da ’ya’yansu a tantagaryar kasa.
“Babu magani, babu abinci kuma babu albashi,” inji Dokta Noorulhaq Yousufzai, wani kwararren likitan yara, wanda ya yi aiki a asibitin na Indira Ghandi na tsawon shekara 28.
“Muna da gadaje 360, amma muna karbar marasa lafiya sama da 500 a kullum, in kuma babu magani, yara za su ci gaba da mutuwa.”
“Idan mutum bai samu isasshen abinci ba, garkuwar jikinsa za ta yi rauni. Tattalin arziki kullum kara tabarbarewa yake, kuma hakan na matukar shafar yara,” inji Yousufzai.
Kazalika, Majalisar Dinkin Duniya ta yi harsashen cewa kimanin mutane miliyan 8.7 ne suka cikin barazanar karancin abinci a kasar da tuni yaki ya kassara.
Bugu da kari, akwai wasu miliyan 24, wadanda kaso 60 ne cikin 100 na mutanen kasar, da suke fama da yunwa, yayin da kaso 95 cikin 100 na mutum miliyan 38 na mutanen kasar ba su da abincin da za su ci.
Kimanin yara miliyan 3.2 ’yan kasa da shekara biyar ne bincike ta nuna suna fama da matsalar yunwa.