Wani matashi dan asalin Jihar Gombe, Aminu Abdulmumini, da yake sana’ar sayar da takalma ya rufe shagonsa ya tafi Legas a kafa don nuna kauna ga jagoran jam’iyyar APC na kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Aminu, mai kimanin shekara 30, wanda dan asalin Karamar Hukumar Gombe ne ya ce kauna ce kawai ta sa shi yin wannan tattaki daga Gombe har zuwa Legas don ya nuna wa Tinubu cewa shi mai kaunarsa ne daga Arewacin Najeriya.
- PDP ta kara wa’adin sayar da fom ga ’yan takara
- Ya gano sulallan Naira miliyan 10 da aka binne a gonarsu ta gado
A zantawarsa da wakilinmu ta wayar salula, matashin ya ce ya share kwanaki 16 a hanya yana tafiya a kafa kuma ya kwana a garuruwa 14, sannan ya kwana daya a daji kafin ya isa birnin Legas.
Ya ce ya fuskanci matsalololi iri-iri a hanya, yayin da wasu kuma suka rika kiran shi a waya suna masa fatan haduwa da ’yan fashin daji ko masu garkuwa da mutane.
Abdulmumini, ya ce akwai wadanda suka kira shi suka ce masa wahalar banza zai sha kuma ma Tinubun ba shi da lokacinsa.
A cewarsa, ya yi fama da ciwon kafa sosai inda kafar ta kumbura ga ciwon jiki, amma duk da haka bai yi nadamar yin tattakin ba, duk da yake har yanzu ba su kai ga ganawa da gwanin nasa ba.
Ya kara da cewa dalilinsa na yin tattakin bai wuce zunzurutun soyayya da yake yi wa Bola Tinubu ba, musamman ganin ya zama Shugaban Najeriya a 2023.
“Idan na hadu da Tinubu, zan gaya masa hanyoyin da zai bi dan cin zabe a yankin Arewa, sannan idan ya ci zabe kar ya manta da yankin,” inji matashin.
Ya ce yanzu haka kusan kwana da 14 a Legas bai samu ganin Tinubun ba, inda aka ce masa yana Abuja.
Sai dai ya ce ya hadu da wata mata da ya kira ’yar arziki mai suna Hajiya Yasmin Binta Saleh, wacce ’yar-ga-ni-kashenin Tinubu ta ba shi wajen kwana kuma take ba shi abinci.