✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tsakanin Kwankwaso da Obi wani zai mara min baya — Atiku

Atiku ya ce tsakanin Kwankwaso ko Obi wani zai mara wa tafiyarsa baya a zabe mai zuwa.

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya ce har yanzu yana tattaunawa da takwaransa na jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso kan yiwuwar goya masa baya a zaben da ke tafe.

Atiku, ya bayyana haka ne cikin wata hira da ya yi da sashen Hausa na BBC, inda ya ce Peter Obi ma suna tattauna kan yiwuwar yin tafiya tare.

Sai dai ya ce abokan hamayyar tasa biyu, ba za su zame masa barazana a zaben da za a yi ba.

“Ba na kallon su a matsayin wata barazana, saboda muna tare. Muna tattaunawa da su, akwai yiwuwar daya daga cikinsu zai dawo tafiyarmu,” a cewarsa.

Game da rikita-rikitar da jam’iyyar PDP ke fama da ita, Atiku ya ce kowace jam’iyyar siyasa na da irin nata matsalolin cikin gida da take fama da su.

“Kowace jam’iyya na da rikicin cikin gida, muna tattaunawa da kowa saboda wasu matsalolin na cikin gida ne, wasu kuma na waje. Amma dai mun shirya tunkarar zabe.

“Zaben yanzu ba irin na da ba ne da Gwamna zai sa a zabi wanda yake so, yanzu makomar zabe na hannun masu kada kuri’a.”

Kazalika, Atiku ya yi alkawarin bude dukkanin iyakokin Najeriya da gwamnatin APC ta rufe da zarar ya lashe zaben Shugaban Kasa.