✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tsakanin kunun kanwa, na tsamiya da koko wanne ya fi lafiya ga jiki?

Lallai da alama santin kunun azumi har yanzu bai sake ka ba dan Zariya

Tambaya daga Alhussain Dakace, Zariya

Amsa: Lallai da alama santin kunun azumi har yanzu bai sake ka ba dan Zariya.

Wannan tambaya zan so a ce akwai ma’aikatan lafiya masu lura da ci-maka wato dietitians da za su karantata su turo mana da amsar ra’ayinsu.

Amma in zan yi karambani zan iya cewa a cikin wadannan ukun, kunun tsamiya zai ciri tuta, sa’annan na kanwa, sa’annan koko.

Amma idan ka bar ni zan iya cewa ’yan uwanmu Fulani masu shan kunun gyada da kunun shinkafa sun fi mu Hausawa
more kunu.

Domin ni a ganina idan aka jera dukkan nau’o’in kunu, kunun gyada ne zai yi zarra kafin na shinkafa, domin ka san musamman shi kunun gyada da hatsi da gyada ake hadawa.

Bari mu koma kan wadancan guda ukun da kake magana bambanci tsakanin kunun tsamiya da na kanwa da koko.

Shi kunu kowane iri ne ya fi koko alfanu domin shi da hatsin gaba dayansa ake hada shi.

Shi kuma koko sai an tace hatsin ake yin sa. To a tsarin kiwon lafiya duk abincin da aka tace, ko aka bare ko aka cire wani bangare na jikinsa aka yi dusa da shi, to kimarsa ta ragu.

Da mukan yi tunanin ai burgewa ce cin hatsin da aka sarrafa ta hanyar barjewa ko tacewa, amma yanzu an gano akwai amfani sosai a dusar da muke cirewa muke ba dabbobi.

To ka ji dalilin da ya sa kunu ya fi koko.

Sai a zo a duba tsakanin kunun kanwa da na tsamiyar su kuma. Wato daya da kanwa ake yin sa, daya kuma da tsamiya.

To a lafiyance, za a iya cewa tsamiya (ko lemon tsami, tun da wasu lemon tsami suke sa wa), sun fi kanwa alfanu ga
jiki saboda sukan samar da nau’in bitaman na ajin C.

Ita kanwa ba mu cika so ana amfani da ita sosai ba saboda ita ma nau’i ne na gishiri. Amma idan ba kullum ake sha ba, jefi-jefi ne, to ba matsala. To ka ji bayananka.

Amma a dage a jarraba shan kunun gyada ma da na shinkafa da sauran
ire-iren kunu, musamman ma na gyada din, wanda kowa, manya da yara za su
iya sha.

Idan ana ba yara za a rika ganin suna cikowa suna sheki.

Sauran nau’o’in kunu da akan yi yanzu a kasar Hausa ko aka aro daga wasu al’adu sun hada da kunun zaki, kunun aya, kunun dankali, kunun acca ga masu ciwon suga da sauransu.

Dukkansu ana sha kuma suna da amfani. Abin dai lura a nan shi ne tsabtarsu. Yawanci idan aka sayo a waje za a iya samun matsalar bacin ciki, amma idan aka hada a gida cikin tsabta da wuya su bata ciki.

%d bloggers like this: