✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsaftar Muhalli: Kotu ta rufe tashar mota da gidan mai a Kano

Kotun ta sake cin tarar masu babura da daidaikun mutane da suka karya dokar.

Wata kotun tafi da gidanka a jihar Kano ranar Asabar ta rufe gidan mai da tashar mota saboda karya dokar tsaftar muhalli ta jihar.

Wuraren da abun ya shafa sun hada da tashar motar Kano Line dake kan titin Zariya, da gidan man Aliko dake unguwar Dakata, a Kano.

Ana yin tsaftar muhallin ne duk Asabar din karshen wata inda ake umartar jama’a su zauna a gida har zuwa karfe 10 na safe domin tsaftace muhallansu.

Alkalin kotun, Auwalu Yusuf Suleiman ne ya yanke hukunci kan wuraren tare da cin su tarar kudi N200,000.

Yusuf Suleman, ya ce an same su da bude wuraren a lokutan da gwamnati ta ce kowa ya zauna a gida don tsabtar muhalli, wanda kuma a cewarsa ya saba da sassa na 98 da 99 na Kudin Tsabtar Muhalli na shekara 2016, na jihar Kano.

Alkalin ya ce sai sun biya tarar da aka yanka musu tare da aikewa da takardar neman afuwa ga Ma’aikatar Muhalli ta jihar, kafin a sake bude su.

Yayin da yake nasa jawabin, Kwamishinan Ma’aikatar Muhalli na jihar Kabiru Ibrahim-Getso, ya koka kan yadda masu baburan Adaidaita Sahu ke karya dokar.

Ya kara da cewa ma’aikatar na shirin horar da jami’an KAROTA don tilasta mutane bin dokar ta tsaftar muhallin.

Kotun dai ta kuma ci tarar masu babura da daidaikun mutane da suka fito ba tare da lokacin fita ya yi ba.