Al’ummar Jihar Kano sun gudanar da salloli na musamman da addu’o’in Alkunut domin neman sauki daga Allah game da halin yunwa da tsadar rayuwa da ake fama su a Najeriya.
Jama’ar jihar, wadanda akasarinsu matasa ne sun gudanar da wadannan addu’o’i ne a wurare daban-daban ne domin samun samun agaji daga Allah kan halin da kasar ke ciki.
Hakan na zuwa ne bayan zanga-zangar gama-gari da aka gudanar a jihar ya rikide zuwa tarzoma da sace-sace da rauni da kuma kisan jama da jami’an tsaro suka yi.
A halin da ake ciki ana shirin yin azumi da kuma addu’o’i na musamman a ranar Litinin 12 ga watan Agusta da muke ciki domin neman samun sauki daga Allah kan daga halin da kasar ke ciki.
- Bata-gari sun yi yunkurin wawushe kaya a Kasuwar Dawanau
- NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Su Gamsu Da Jawabin Tinubu Ba
Daya daga cikin wadanda da suka shirya taron addu’o’in, Mubarak Ibrahim ya ce, “an zabi lokacin ce a matsayin Ranar Add’io’i ta Kasa.
“Za mu yi karin addu’o’i da yin azumi, muna rokon Allah Ya gafarta mana zunubanmu, Ya yi mana rahama.
“Mun yi imani da karfin addu’a, kuma shi ne abin da ya kamata mu rike wannan lamari, maganar da shugaban kasa ya yi ba ta yi wa jama’a dadi ba kowace fuska.
“Abin da muka tsara shi ne za mu fara daga ranar Juma’a a duk jihohin kasar nan inda za mu yi ta karatun Alkur’ani har zuwa ranar Asabar, sannan mu dauki azumi ranar Litinin,” in ji shi.