Hukumar Kwastam ta Kasa, ta fara rabon kayan abincin da ta kwato daga hannun masu fasa kwauri don rage yunwa da tsadar rayuwa da ake fama da su a Najeriya.
Da yake jawabi a wajen kaddamar da rabon kayan abincin a Legas a ranar Alhamis, Kwanturolan hukumar, Mista Wale Adeniyi, ya ce gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin raba kayan abincin da suka kwato.
- ’Yan sanda sun hallaka dan bindiga yayin karbar kudin fansa
- NAJERIYA A YAU: Tallafin Da ’Yan Najeriya Ke Bukata
Ya ce hukumar ta hada kai da wasu hukumomi domin raba kaya abincin ga ’yan Najeriya.
A cewarsa kafin a bai wa mutum kayan abincin, dole ne ya gabatar da lambar shaidar ɗan kasa ta (NIN) don cin gajiyar rabon.
“Za mu hada hannu da masu sana’ar hannu, malamai, kungiyoyin addinai da sauran ‘yan Najeriya a fannin ayyukan kwastam.
“Manufar raba wannan kayan shi ne rage radadin halin da ake ciki a yanzu na yunwa.”
Ya ce matakin na daga cikin kokarin gwamnatin tarayya ke yi na tabbatar da rage farashin kayan abinci da suka yi tashin gwauron zabi a fadin kasar nan.
“Mun hada kai da sauran hukumomin gwamnati, don jagorantar rabon kayan abinci.
Adeniyi, ya ce daga cikin kayan abincin da hukumar za ta raba sun hadar da shinkafa, wake, taliya, macaroni, man gyada, man ja, masara, dawa, da sauran dangin kayan abinci masu yawa.
Wannan na dai na zuwa ne bayan da ‘yan Najeriya ke ci gaba da kokawa kan yadda farashin kayayyaki suka tsefe a kasar.