✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsadar Rayuwa: Komawa Ga Allah Ne Mafita — Rijiyar Lemo

Malamin ya ce babu wani shugaba da zai iya kawo karshen halin da ake ciki a Najeriya a yanzu.

Sheikh Dokta Ibrahim Muhammad Rijiyar Lemo, Kano, ya bayyana cewa komawa ga Allah ne kadai mafita dangane da halin kuncin rayuwa da ake fuskanta a Najeriya.

Rijiar Lemo, ya ce ba yadda za a yi Allah ya yaye halin da aka ciki wannan hali na kuncin da ake ciki matukar al’umma ba su koma gare shi ba.

Ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi a Gombe, a wajen taron bita na kwana daya da Kungiyar Jama’atul Izalatil Bid’ah, ta shirya wa malamai da za su gabatar da tafisiri a watan Azumi mai zuwa.

A cewarsa babu wani shugaba da zai iya kawo karshen matsin rayuwar da ake fuskanta ta kowace hanya idan ba Allah ba.

Ya kara da cewa ko da an dawo da tallafin mai da aka cire, matukar al’umma ba su koma ga Allah babu wani sauyi da za a samu.

Malamin ya gargadi mutane kan zage-zagen shugabanni, face bukatar kowa ya gyara tsakaninsa da mahallacinsa.

“Idan muka koma ga Allah da yakinin cewa Allah ne mafita za a samu saukin rayuwa,” innji shi.

Sannan ya ce idan za a koma ga Allah a yi ta addu’a Allah zai ji kukan bayinsa sannan kuma ta tausaya a samu sauki.

Kazalika, ya yi kira ga al’umma da su jajirce wajen yin addu’a da ikilasi da yakinin samun sauki daga Ubangiji.