A yayin da Sallar Layya take kara matsowa, jama’a sai kokawa suke yi kan tsadar rayuwa a Jihar Gombe, duk da biyan albashi da gwamnatin jihar ta yi.
A kan haka ne wakilinmu ya zaga wasu kasuwannin dabbobi a garin Gombe domin ganin irin wainar da ake toyawa inda ya iske masu sayen dabbobin layya da masu sayarwa duk kokawa suke yi.
Wani wanda wakilinmu ya yi kicibus da shi ya je sayan ragon layya a garin, ya ce sayen dabbobi a bana sai mutum ya yi ta maza.
Kasuwar Pantami
Wani dan kasuwa mai sayar da kananan dabbobi a Kasuwar Pantami, Abba Muhammad, ya shaida wa wakilin namu cewa raguna sun yi tsada sosai a bana, sannan ya dora laifin hakan a kan tashin gwauron zabon farashin abincin dabbobi.
Abba ya koka cewa kudin abincin dabbobi ya ninku a bana inda ake sayar da buhun kowar wake a kan N4,000 sabanin bara da ake sayarwa N2,000 zuwa N2,200.
Kaikayin dawa da aka sayar N1,500 a bara kuma ya koma N3,000 a bana, Buhun dusan N3,000 a bara kuma yanzu ya tashi zuwa N6,000.
Ya ce baya ga tsadar abincin, karancin dabbobin ma ya taimaka wajen kawo tsadarsu a bana.
A cewarsa, ragon N50,000 a bara, ya kai N90,000 zuwa N100,000 a bana, na N30,000 zuwa N40,000 a bara kuma a bana sun kai 70,000.
Tashar Dukku
Aminiya ta kuma leka Kasuwar Shanu da ke Tashar Dukku, inda ta jiyo farashin shanu.
Wakilinmu ya gano cewa farashin saniya matsakaiciyar da a ake sayarwa N130,000 a yanzu a kasuwar, a bara ba ta wuci N60,000 zuwa N70,000 ba, wadda kuma ake sayarwa N200,000 yanzu kuma ba ta wuce N120,000 ba a bara.
Masu sayen raguna
Wani da muka zanta da shi a lokacin da ya je sayan rago a garin, Ibrahim Muhammad, ya ce sayen dabbobi a bana sai mutum ya rufe ido.
A cewarsa, ya je kasuwar da niyar sayen ragunan N40,000 guda uku, amma idan ya saya biyu ma babu canjin da zai rage a hannunsa.
ganin cewa an yi albashi, mun zanta da wasu ma’aikata game da yiwuwar yin layyarsu.
Inuwa Ya’u ya ce shi ko abinci babu a gidansa, don haka ba zai kwashe albashinsa ya sayi dabbar layya ba daga baya ya koma yana raba idanu.
Amma Mansur Abubakar ya ce shi ko saboda yara sai ya yi yanka, kuma da ba a biya albashi ba da bashi zai nema.