✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsadar abinci na barazanar kawo yunwa a Najeriya —Gambari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na jagorantar zaman Majalisar Samar da Abinci na Kasa (NFSC), sakamakon hauhawar farashin kayan abinci a Najeriya da ke barazanga ga…

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na jagorantar zaman Majalisar Samar da Abinci na Kasa (NFSC), sakamakon hauhawar farashin kayan abinci a Najeriya da ke barazanga ga wadatuwar abinci a kasar.

A baya-bayan nan an samu hauhawar farashin kayan abinci a Najeriya, yayin da ambaliya ke barnata amfanin gona a sassan kasar.

Da yake jajanta wa wadanda suka yi asara iftila’in, Buhari ya ce an yi asarar sama da Naira biliyan biyar na amfanin gona a Jihar Kebbi kadai.

Ya kuma ce ambaliyar da ake samu a bana na barazana ga yunkurin gwamnati na samar da wadaccen abinci, musamman shinkafa a cikin gida da kuma fitarwa zuwa wasu kasashe.

– Barazanar karancin abinci – 

A jawabinsa a wurin taron taron Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Ibrahim Gambari ya ce, “tashin farashin kayan abinci na baya-bayan nan na barazanar kawo karancin abinci a Najeriya”.

Gambari ya jaddada muhimmancin hadin kan masu ruwa da tsaki domin shawo kan matsalar da ke tunkarowa musamman a wannan lokaci da ake fama da matsalar COVID-19 da karancin ababen more rayuwa.

Ya kuma bukaci mahalarta taron da su hada su yi aiki kafa-da-kafa domin tabbatar da samuwar isasshen abinci.

“Noma babban abun da gwamnati ta ba wa muhimmanci ne sannan yana da tasiri wurin kawo cigaban kasa”, inji shi.

Ya ci gaba da cewa, “Jiya (Laraba) ofishina da shugabananin majalisar mun tattauna da kungiyoyin masu sayar a kayan abinci domin gano abin da ya kawo tashin farashin kayan masarufi domin a yi wa tufkar hanci.

“Duk da cewar ana bayyana wasu dalilai, an shaida mana cewa tsadar na raguwa saboda shigowar sabbin hatsin da ake girbewa”, inji shi.

Gwamnoni shida daga cikin bakwai da ke Majalisar na halartar taron tare da wasu ministoci da manyan jami’an gwamnati.

Mahalartan sun hada da Mataimakin Shugaban Majalisar, Gwamann Kebbi, sai kuma Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Legas; Mohammed Badaru Abubakar na Jigawa; Simon Lalong na Filato; Darius Ishaku na Taraba; da kuma Dave Umahi na Jihar Ebonyi.