✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Trump zai gana da Kim Jong-un karo na biyu

Fadar Shugaban Kasar Amurka ta sanar da cewa Shugaban Amurka Donald Trump zai gana da takwaransa na Koriya ta Arewa Kim Jong-un karo ba biyu.…

Fadar Shugaban Kasar Amurka ta sanar da cewa Shugaban Amurka Donald Trump zai gana da takwaransa na Koriya ta Arewa Kim Jong-un karo ba biyu.

Mai magana da yawun Fadar White House, Sarah Sanders ce ta bayyana haka, inda ta ce a karshen watan Fabrairu ne shugabannin biyu za su gana a karo na biyu.

Haka kuma Shugaba Trump ya gana da Mataimakin Shugaban Jam’iyyar Workers Party ta Koriya ta Arewa Kim Yong-chol a faɗar White House.

Sanders ta nanata cewa taron da za a bayyana inda za a gudanar da shi daga baya, Shugaba Trump yana matukar buri da shaukin ganawar da Shugaba Kim.

Idan ba a manta ba, Shugaba Trump ya yi ganawar farko da takwaransa na Koriya ta Arewa Kim Jong-un a kasar Singapore ne a ranar 12 ga watan Yulin bara inda suka amince da batun dakatar da shirin makamashin nukiliyar Koriya ta Arewa.

Sun yi ganawar ce domin kokarin da ake yi na ganin an kauce wa barkewar Yakin Duniya na Uku, wanda ake ganin cewa yaki ne na makamin kare-dangi, wanda Koriya ita ma ta mallake shi, kuma ita ce ake ganin za ta iya rufe ido ta kai wa kasashen Yamma hari da shi.

Bayan wancan tattaunawar, Shugaban Kim ya ce,  “A gaskiya mun sha kwan-gaba-kwan-baya  kafin mu kai ga samun nasarar  ganawa da juna. Amma dukanmu muna da yakinin cewa za mu samu nasarar abin da muka sa a gaba.”