✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Trump na iya jefa Amurka cikin hadari – Sanata Coker

A yayin da kasar Amurka da Koriya ta Arewa ke cigaba da nuna juna da yatsa, inda Shugaban Amurka Donald Trump ya yi gargadin cewa…

A yayin da kasar Amurka da Koriya ta Arewa ke cigaba da nuna juna da yatsa, inda Shugaban Amurka Donald Trump ya yi gargadin cewa hanya daya ce ta rage ayi amfani da ita wajen Ladabtar da Koriya ta Arewar, bayan tsawon shekaru 25 da aka dauka ana neman tattaunawa da ita kan makamin Nukiliya.

daya daga cikin manyan ‘yan Majalisar Dattawan Amurka, Bob Coker ya raba gari da shugaban kasar, Donald Trump, inda ya ce rashin hankalin shugaban na iya jefa Amurka cikin mummunan hadari.

Sanata Bob Coker ya bayyana fadar gwamnatin Amurka a matsayin wurin kula da kananan yara, inda ya bayyana cewa Shugaba Trump na iya jefa Amurka cikin yakin duniya na uku saboda rashin iya tafiyar da mulki.

Koda yake Sanata Coker, ya bayyana Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Red Tillerson da Sakataren Tsaro, Jim Mattis da Babban Hafsa a fadar shugaban kasa, John Kelly a matsayin wadanda ke kare Amurka daga fadawa cikin rikici.

A yayin da Shugaba Trump ke maida martini, ya bayyana cewa Sanatan na furta wadannan kalamai ne sakamakon kin goyon bayan sake tsayawa takararsa da kuma nada shi a matsayin Sakataren Harkokin Waje.

A wannan makon ne Shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jung Un ya sanar da cewa kasar tasa ta yi nasarar kera wani makami mai linzami da zai iya lashe nisan zangon kilomita dubu uku. Amma Trump ya yi gargadin cewa, Amurka za ta iya kawo karshen Koriyar matukar ta ci gaba da barazanar far-ma yankinta.