Ejent din dan kwallon Golden Eaglets bictor Osimhen mai suna Shira Yusuf ya karyata jita-jitar da ake bazawa cewa dan kwallon ya kulla yarjejeniya da kulob din Tottenham na Ingila.
Osinhen wanda ya zura kwallo 10 a gasar cin kofin matasa na duniya na ’yan kasa da shekara 17 (U-17) da aka kammala kwanan nan a Chile kuma ya taimaki Najeriya ta lashe kofin karo na biyar, kulob da dama ne aka ruwaito suke zawarcinsa a Ingila ciki har da na Tottenham.
Jim kadan bayan an kammala gasar ce aka ba dan kwallon kyautar takalmin zinare, watau na dan kwallon da ya fi zura kwallaye a rag. Osimhen kuma ya kafa sabon tarihi na babu wanda ya taba zura kwallaye 10 a raga a gasar sai a wannan karo.
Shira Yusuf ya ce “babu wata yarjejeniya da muka kulla da kulob din Tottenham na Ingila, shaci-fadi ne kawai. bictor Osinmhen dai yana bukatar hutu, bai kamata a rika yawo da hankalin dan kwallon a kan yiwuwar komawarsa wani kulob ba a Ingila a halin yanzu.”
Ya ce “yanzu haka dan kwallon yana Legas amma abin mamaki sai muka jin labarin wai ya sanya wa kulob din Tottenham na Ingila hannu, wannan ba gaskiya ba ne.”
“A gaskiya akwai kulob da dama a Nahiyar Turai da yanzu haka suke rububi a kan dan kwallon, kuma kawo yanzu ba mu yanke shawarar inda zai tafi ba har sai mun tuntube shi kuma ya amince, amma idan lokaci ya yi kowa zai sani,” inji Shira Yusuf.
Kamar yadda aka rida yada jita-jita, kulob da dama ne a Ingila suka rika zawarcin Osimhen ciki har da Manchester United da Arsenal da Liberpool da Manchester City da kuma na Tottenham.
Tottenham ba ta kulla yarjejeniya da dan kwallon Eaglets Osimhen ba – Shira Yusuf
Ejent din dan kwallon Golden Eaglets bictor Osimhen mai suna Shira Yusuf ya karyata jita-jitar da ake bazawa cewa dan kwallon ya kulla yarjejeniya da…