✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gano bututun satar mai a kusa da sansanin soji

A kwananin bayan an gano bututai 58 na satar mai a jihohin Delta da Bayelsa

An sake gano wani bututun da ake amfani da shi wajen satar danyen mai a kusa da wani sansanin sojoji a Karamar Burutu ta Jihar Delta.

Kamafanin TSSNL wanda gwamnatin Najeriya ta bai wa kwangilar tsaron bututun mai, wanda tsohon shugaban ’yan tarastsin Neja Delta, Government Ekpemupolo Tompolo, yake jagoranta ne ya gano wannan haramtaccen butun mai.

Tompolo ya bankado yadda bututun ke satar danyen mai daga bututun Trans-Forcados, wanda gwamnati ke amfani da shi wajen fitar da mai zuwa kasashen waje, a kusa da sansanin sojoji da ke tashar Ogulagha a karamar hukumar Burutu.

Kamfanin ya gano haramcacen bututun ne kimamin mako guda bayan ya gano wasu bututai 58 wadanda ake amfani da su wajen satar mai a jihohin Delta da Bayelsa.

Idan ba a manta ba a baya rahotanni sun bayyana yadda kamfanin TSSNL ya gano wani haramtaccen bututun mai mai tsawon kilomita hudu da aka jona a jikin bututun Trans-Forcados domin satar mai.

Zargin NNPC da jami’an tsaro

Jaridar Vanguard na zargin kamfanonin hakar mai da ke aiki a Najeriya da hada baki da masu satar man da wasu gurbatattun jami’an tsaro da na kamfanin NNPC wajen satar mai.

Wata kungiyar mazauna yankin Neja Delta na barazanar gurfanar da kamfanin NNPC da Shell saboda yadda ake fasa bututun man Najeriya ana sace man tare da gurbata musu muhalli.

Bututun kamfanin Shell

Kamfanin hakar mai na Shell ne dai ke amfani da Tashar Danyen Mai ta Forcados da ke Ogulagha, wadda take fitar da gangar mai 400,000 a kullum.

Forcados shi ne bututun mai mafi girma na biyu, a yankin Neja Delta, bayan bututun Bonny.

Daraktan kungiyar da ke sanya ido kan harkar mai, ya ce suna samun labarin satar man da dama a Neja Delta amma abin da yafi dauke musu hankali shi ne yadda ake satar danyen man ta tashar ruwa.

Ya ce an yi akalla shekaru tara ana satar man Najeriya kuma babu wanda zai iya cewa ga hakikanin lokacin fara irin wannan aika-aika.

Don haka ya ce suka zura ido kan abin da kamfanin Shell da NNPC za su yi.