✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Titin Kano-Maiduguri: Gwamnati ta ba da wa’adin wata 10 a kammala

Nan da watan Disamba ake son dan kwangilar ya kammala aikin, inji minista.

Gwamnatin Tarayya ta bukaci kamfanin da ke aikin gyaran titin Kano zuwa Maiduguri da ya bi ta Shuwarin a Jihar Jigawa da ya kammala aikin nan da watan Disamba.

Da yake kiran a yayin rangadin duba aikin a ranar Juma’ar a Karamar Hukumar Wudil, Jihar Kano, Minista a Ma’aiktar Ayyuka da Gidaje, Abubakar Aliyu, ya ce aikin da aka bayar shekaru da yawa da suak gabata an yi watsi da shi, amma ya sami kulawa sosai tun zuwan Shugaba Buhari.

Ya kara da cewa aikin yana samun gagarumar cigaba idan aka kwatanta da abin da ya gani yayin ziyararsa ta karshe.

Don haka ya yi kira ga dan kwangilar da ya yi duk mai yiwuwa don kammala aikin nan da watan Disamba.

Ministan ya yaba da inganci da kuma saurin aikin titin mai tsawon kilomita 101, yana mai cewa, “wannan babbar nasara ce kuma ba za mu yi kasa a gwiwa ba, za mu ci gaba da ingiza su har sai sun kammala a cikin lokaci.

“Na sha kawo ziyarar duba aikin nan, kuma mung a mahimmancin ziyarar a-kai-a-kai da irin nasarorin da aka samu ya zuwa yanzu.

“Da ba a ziyartar dukkan wuraren da ake aikin da ’yan kwangila sun yi kasa a gwiwa.

“Amma yayin da muke zuwa ziyarar akai-akai,‘ yan kwangilar koyaushe suna kan alƙawarinsu saboda sun san za mu iya zuwa kowane lokaci ko da ba da sanarwa.

“Mun aba da kudin aikin, saboda haka babu dalilin yin jinkiri; a baya suna fuskantar kalubale, amma yansu dade da magance matsalar.

“Kwanan nan mun kara aikin, kuma hakan ya faru ne saboda yawan ziyarar da muke yi, lokacin da ya kawo bukatar karawa.

“Ba mu bata lokaci ba saboda mun ga abin da yake korafi a kai, kuma nan take muka amince. Wannan yana daga cikin dalilan da ke ba su kwarin gwiwar yin aikin da sauri.

“Gaskiya mun gamsu da matakin da ingancin aikin, amma har yanzu muna rokon su da su kara himma wajen isar da sako da kuma bai wa masu ababen hawa damar jin dadin hanyar.”

Ministan ya ce ba zaina ziyrar wurin ba har ya tabbata sai dan kwangilar ya kammala aikin a kan kari.