✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Titin jirgin kasa daga Kano-Nijar zai ci Dala biliyan biyu

Titin jirgin zai ratsa garuruwa takwas a jihohin Kano, Jigawa da Katsina

Gwamnatin Tarayya ta amince da bayar da kwangilar gina hanyar jirgin kasa daga Kano-Katsina-Jibia zuwa Maradi a Jamhuriyar Nijar a kan Dala biliyan 1.9. 

Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana haka bayan Zaman Majalisar Zartaswa ta Kasa da Shugaba Buhari ya jagoranta, a fadarsa da ke Abuja a ranar Laraba.

Hanyar mai tsawon kilomita 248 da ke cikin kasafin kudin 2018 za ta ratsa garuruwa takwas a jihohin Kano, Jigawa da Katsina a Najeriya da kuma jiha daya a Jamhuriyar Nijar.

Titin zai tashi daga Kano, ya bi ta Dambatta da Kazaure da Daura da Mashi da Katsina da Jibia sannan ya tsaya a Jihar Maradi, Jamhuriyar Nijar.

Ana ganin gina hanyar jirgin zai saukaka jigilar danyen mai daga Jamhuriyar Nijar zuwa matatar man fetur da aka ginawa a kan iyakokin kasashen biyu, kamar yadda aka yi yarjejeniya makon jiya.

  • Sauran abubuwan da aka amince

Amaechi ya kuma ce an amince ma’aikatar sufurin ta kera mota mai karfin daukar nauyi ton 15 a kan kudi N3,049,544,000 don taimakawa idan an yi hatsari da kuma jiran-ko-ta-kwana.

Haka nan kuma, Ministan Ayyuka, Babatunde Fashola, ya bayyana wa ‘yan jarida cewa an amince da yin kwangilar hanyar Umuahia-Bende-Ohafia a Jihar Abia, a kan Naira biliyan 12.

Ministan Watsa Labarai da Al’adu, Lai Mohammed, ya ce an amince da sayen kwamfutoci laptop 1,800 domin koyar da amfani da kwamfuta wajen jarabawa a makarantun horaswa na Hukumar Hana Fasa Kauri (NCS) da ke Gwagwalada da Legas da Kano a kan biliyan N351,540,000.

Zaman ya kuma amince da kashe biliyan N197,843,100 don a fadada kimiyyar tafiyar da kudaden Hukumar Hana fasa kwaurin kasa.

Ya kuma amince da bukatar Minista a Ma’aikatar Man Fetur, Timipre Sylva, na cikon kudin gina ofishin PTF a Abuja.