✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tirelar siminti ta fado daga Gadar Sama a Kano

Wata tirelar dakon siminti ta fado daga kan gadar sama da ke Kofar Kabuga da ke Kano.

Wata tirelar dakon siminti ta fado daga kan gadar sama da ke Kofar Kabuga a Kano.

A safiyar Litinin ne dai tirelar dakon siminti ta yi hatsari ne a gadar sama da ke Karamar Hukumar Gwale a Jihar Kano.

Daga bisani motar ta fara neman fadowa daga saman gadan, lamarin da ya jefa jama’a cikin zullumi.

Wasu mazauna unguwar Kabuga sun ce tsautsayin ya auku ne bayan motar ta fito daga titin Tal’udu.

Zuwa lokacin da muka samu labari dai babu bayani game da abin da ya haddasa hatsarin.