✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tirela ta take mutum biyu sun mutu a Benuwe

A safiyar yau Talata wata babbar mota kirar tirela ta yi sanadiyyar rasuwar mutum biyu bayan ta take su a sabuwar hanyar Otukpo da ke…

A safiyar yau Talata wata babbar mota kirar tirela ta yi sanadiyyar rasuwar mutum biyu bayan ta take su a sabuwar hanyar Otukpo da ke Makurdi babban birnin jihar Benuwe.

Kwamandan Hukumar kiyaye hadurra ta Kasa (FRSC) na jihar Benuwe, Aliyu Baba, ne ya tabbatarwa majiyarmu hakan.

Aliyu, ya ce wadanda suka rasa rayukan na su, su ne wani dan achaba da wata mace fasinja da ya dauka. Hadarin ya faru ne da misalin karfe 8:40 na safe.