✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tirela makare da kankana ta yi hatsari a Jigawa

Motar ta yi hatsari ne bayan ta kwace a yammacin ranar Laraba a kusa da kauyen Katanga da ke Jihar Jigawa, a hanyarta ta zuwa…

Wata tirela makare da kankana ta yi hatsari tare da jikkata mutum shida, ciki har da direbanta da yaron motarsa a Jihar Jigawa.

Motar ta yi hatsari ne bayan ta kwace a yammacin ranar Laraba a kusa da kauyen Katanga da ke Karamar Hukumar Kiyawa, a hanyarta ta zuwa garin Fatakwal, Jihar Ribas.

Mutum shidan da suka samu raunukan na cikin motar ne a lokacin da ta kwace ta fadi, inda hudu daga cikinsu suka ji munanan raunuka.

Ganau sun ce an garzaya da su asibiti, amma daya daga cikin mutanen tirelar da ya farfado ya ce za su kai kankanar ce domin sayarwa a Fatakwal.

Wani ganau, Danlami Gambo, wanda shi ne mai ganin Makarantar Firamaren Katanga Primary ya ce karar faduwar motar ya ji, shi ne suka ruga zuwa inda ta fadi domin kai dauki.

Ya bayyana kaduwa da hadarin, domin a cewarsa ba su taba ganin mai muninta ba a kan hanyar.