✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu zai yi wa ’yan Najeriya jawabi ranar Litinin

Zai yi jawabin da karfe 7:00 na safe

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, zai yi wa ’yan Najeriya jawabi ranar Litinin, albarkacin ranar Dimokuradiyya ta bana.

Wannan dai shi ne zai kasance jawabin farko da Tinubu zai yi wa ’yan kasa tun bayan rantsar da shi a mukamin ranar 29 ga watan Mayun da ya gabata.

Zai yi jawabin ne da misalin karfe 7:00 na safe, kamar yadda Daraktan Yada Labarai na Fadar Shugaban Kasa, Abiodun Oladunjoye, ya sanar a cikin wata sanarwa ranar Lahadi.

Ya yi kira ga kafafen yada labarai na rediyo da talabijin da su jona da Gidan Talabijin na Kasa (NTA) da kuma Gidan Rediyon Tarayya don watsa jawabin kai tsaye.