Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, zai yi wa ’yan Najeriya jawabi ranar Litinin, albarkacin ranar Dimokuradiyya ta bana.
Wannan dai shi ne zai kasance jawabin farko da Tinubu zai yi wa ’yan kasa tun bayan rantsar da shi a mukamin ranar 29 ga watan Mayun da ya gabata.
- Betara da Gagdi sun janye wa Tajuddeen takarar Shugabancin Majalisar Wakilai
- Nigeria Air: Ko sisi ba mu kashe ba wajen dauko hayar jirgin Habasha – Sirika
Zai yi jawabin ne da misalin karfe 7:00 na safe, kamar yadda Daraktan Yada Labarai na Fadar Shugaban Kasa, Abiodun Oladunjoye, ya sanar a cikin wata sanarwa ranar Lahadi.
Ya yi kira ga kafafen yada labarai na rediyo da talabijin da su jona da Gidan Talabijin na Kasa (NTA) da kuma Gidan Rediyon Tarayya don watsa jawabin kai tsaye.