Gwamnatin Tarayya ta ce za ta tattauna da shugabannin kungiyoyin kwadago da misalin karfe 3:00 na ranar Litinin saboda kaucewa shiga zanga-zangarsu ranar Talata.
Ministan Kwadago, Simon Lalong, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da safiyar Litinin.
Ya ce bai kai ga zama da kungiyoyin kwadago ba kafin yau [Litinin], amma bai samu cikakkun bayanai daga sauran bangarorin da ya kamata ba.
Lalong ya kuma yi kira ga kungiyoyin kwadago na NLC da TUC da su roki abokan huldarsu don su dakatar da shirin zanga-zangar ba yanzu ba.
A makon da ya gabata ne dai NLC da TUC suka sanar da fara zanga-zanga ranar Talata domin sake matsa wa gwamnati lamba kan manufofinta na tattalin arziki da suka ce sun yi wa ’yan kasa tsauri.