Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, a ranar Alhamis zai bi sahun sauran kasashen duniya a birnin Paris na kasar Faransa, domin sanya hannu a kan sabuwar yarjejeniyar kudi ta duniya.
Babban Hadimin Shugaban a bangaren Ayyuka na Musamman da Yada Labarai, Dele Alake ne ya sanar da hakana a cikin wata sanarwa ranar Litinin.
Wannan ne dai karo na farko da Shugaban zai yi tafiya zuwa kasar waje, tun bayan rantsar da shi a watan da ya gabata.
Tinubu dai zai sami rakiyar mambobin Kwamitinsa Shugaban Kasa na Tattalin Arziki da kuma manyan jami’an gwamnati.
Taron dai zai mayar da hankali wajen duba hanyoyin sake farfado da tattalin arziki tun bayan mummunar illar da annobar COVID-19 ta yi wa kasashen duniya.
Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ne dai zai jagoranci taron wanda za a yi a Palais Brongniart.
Za a yi taron ne tsakanin ranakun 22 da 23, kuma zai mayar da hankali wajen magance kalubalen, musamman ta bangaren samar da makamashi.
Dele Alake dai ya ce ana sa ran Shugaba Tinubu zai dawo Abuja a ranar Asabar.