✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Filato: An sanya dokar hana fita ta awa 24 a Mangu

An sanya dokar ce bayan samun wasu hare-hare a yankin

A sakamakon zaman dardar da ake ciki a Karamar Hukumar Mangu da ke Jihar Filato. Shugaban Karamar Hukumar, Markus Artu, ya sanya dokar hana zirgazirga ta tsawon awa 24.

Shugaban ya sanya dokar ce a wata sanarwa da ya fitar mai dauke da sanya hanunsa., ranar Litinin.

Sanarwar ta yi bayanin cewa dokar ta kunshi hana zirga-zirgar dukkan ababen hawa na awa 24 a yankin, har sai abin da hali ya yi.

“Ba a son ganin kowa yana zirga-zirga a yankin, sai dai jami’an tsaro ko kuma wadanda aikinsu ya zama wajibi ga al’umma,” in ji sanarwar.

Matakin sanya dokar na zuwa ne bayan da aka sami wasu munanan hare-hare kwanakin baya.

Hare-haren dai sun yi sanadin asarar rayukan sama da mutum 150 da dukiyoyi masu tarin yawa.