✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu zai tafi Faransa taro

Tinubu da mai ɗakinsa da kuma wasu jami'an gwamnatin Najeriya za su shafe tsawon kwanaki uku a Faransa.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai bar Abuja ranar Laraba domin kai ziyara ƙasar Faransa.

Shugaba Emmanuel Macron ne, ya gayyaci tare shi tare da mai ɗakinsa, Remi Tinubu.

Ziyarar, wadda za ta ɗauki tsawon kwanaki uku, za ta mayar da hankali ne kan ƙarfafa dangantakar siyasa, tattalin arziƙi, da al’adu tsakanin ƙasashen biyu.

Har ila yau, ƙasashen biyu za su duba yiwuwar haɗin gwiwa musamman a fannonin noma, tsaro, ilimi, kiwon lafiya, hulɗar matasa, aikin yi, da ƙirƙire-ƙirƙire.

Shugaba Macron da matarsa Brigitte, za su tarbi Tinubu da mai ɗakinsa a ranar Alhamis a fadar shugaban ƙasar, Palais de l’Élysée.

A yayin ziyarar, shugabannin biyu za su tattauna hanyoyin ƙara ɓullo da shirin musayar matasa, domin bunƙasa basirarsu a fannonin ƙirƙire-ƙirƙire, kasuwanci, da harkar jagoranci.

Za su kuma yi taro kan harkokin siyasa da diflomasiyya game da kuɗaɗe, ma’adinai, cinikayya, sanya hannun jari, da sadarwa.

Hakazalika, za su halarci taron Majalisar Kasuwancin Faransa da Najeriya, wanda ke kula da shigar kamfanonin masu zaman kansu wajen ci gaban tattalin arziƙin ƙasashen biyu.

Uwargida Brigitte Macron da Uwargida Oluremi Tinubu za su tattauna kan yadda za su ƙara inganta rayuwar mata, yara, da masu ƙaramin ƙarfi.

Shugaba Tinubu da matarsa za su halarci taron cin abincin dare na musamman tare da shugaban Faransa ya shirya.

Za su kasance tare da manyan jami’an gwamnatin Najeriya, na tsawon kwanakin da za su yi a ƙasar.