Hukumar Samar da Wutar Lantarki a Yankunan Karkara (REA) ta ce Gwamnatin Shugaban Kasa Bola Tinubu za ta samar da lantarki mai amfani da hasken rana don rage wa ’yan Najeriya radadin cire tallafin man fetur.
Shugaban hukumar, Injiniya Ahmad Salihijo ne ya bayyana hakan, lokacin da yake duba aikin samar da lantarkin ta hanyar hasken rana a kasuwar Ayegbaju da ke Jihar Osun.
Ya ce ’yan Najeriya za su amfana da aikin ne a gidajensu da wuraren kasuwanci, domin rage dogaron da ae yi da wutar lantarki kacokam a kasar.
Salilhijo ya kuma ce tun da farko an kirkiro aikin ne domin fadada hanyoyin samun ingattacciyar lantarki.
Hakan, a cewarsa zai kuma taimaka wajen rage yawan gurbatacciyar iskar da ake fitarwa ta hanyar amfani da injinan janareta.
Mun zo ofishinmu na shiyya ne da ke nan Osun, sai muka yanke shawarar yin ’yar kwarya-kwaryar ziyara domin ganin yadda aikin lantarkin ke tafiya a kasuwar kasa da kasa ta Ayegbaju a Osogbo,” in ji Salihijo.
A ranar da aka rantsar da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ce dai ya sanar da janye tallafin man fetur gaba daya, inda ya yi alkawarin fito da hanyoyin da za su taimaka waje rage wa ’yan kasa radadin da matakin zai haifar musu.