✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu zai kori duk ministan da ya gaza katabus — Ajuri Ngelale

Mai magana da yawun shugaban kasar, ya ce a shirye Tinubu yake ya sallami duk ministan da gaza kai batensa.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale, ya ce shugaba Bola Tinubu a shirye yake ya kori duk wani minista da ya gaza a aikinsa.

Ana iya tuna cewa an zargi tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da barin da yawa daga cikin ministocinsa a kan mukamansu duk da korafe-korafen rashin katabus har na tsawon shekara takwas.

Amma da yake magana yayin tattaunawa da Gidan talabijin na Channels, a ranar Litinin, Ngelale ya ce rashin cimma burin da aka sanya a gaba na iya sa Tinubu ya sallami kowane minista.

“Shugaba Bola Tinubu mutum ne da yarda da samar da sakamako. Ya ce ‘Na san dalilin da ya sanya na baku minista, na san abin da nake so ku cimma, ba na tsammanin ku yi wani abu na daban. Kuma na kayyade lokacin da na ke ku cimma abin da ake so.

“Tambayar a yanzu ita ce ta aiwatar da doka kuma shugaban kasa ya nuna kamar yadda ya yi a lokacin da yake gwamnan Legas, cewa ba ya tsoron korar kowa.

“Ba mutum ne da ke tsoron sanya takunkumi ba don samun sakamakon da yake so, a karshe, idan wannan gwamnatin ta gaza, ba za su ce minista ya gaza ba ko kuma wasu ministocin sun gaza. Za su ce Shugaba Bola Tinubu ya gaza, kuma ba zai yarda hakan ta faru ba.”

“Tabbas idan minista ba ya samar da abin da ake so zai iya sallamarsa tun kafin a je ko ina, babu tantama a wannan.”