Shugaba Bola Tinubu, zai kai ziyara birnin Riyadh na Kasar Saudiyya domin halartar taron kasashen Larabawa da Afirka a ranar 10 da 11 ga watan nan na Nuwamba.
Mai magana da yawun shugaban, Ajuri Ngelale, ya ce a yayin taron, Tinubu zai tattauna kan batutuwa da suka shafi huldar tattalin arziki tsakanin yankunan da harkar noma da kuma yaki da ta’addanci.
- Yadda ’Yan Najeriya Za Su Kwaci Hakkinsu Daga Gwamanti Cikin Sauki
- Isra’ila ta dakatar da Ministan da ya bukaci a ragargaza Gaza da nukiliya
Sauran su ne batun inganta harkokin kasuwanci da zuba jari a tsakanin Saudiyya da nahiyar Afirka.
A cewarsa hadimin shugaban kasar, halartar taron wani yunkuri ne na bunkasa tattalin arzikin Najeriya da kuma jawo hankalin kasashen waje.
Ngelale ya ce a matsayin Tinubu na shugaban hukumar gudanarwar Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Yammacin Afirka (ECOWAS) zai kasance kan gaba a taron wajen bayar da shawarwarin zurfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen yankuna biyu.
“Tabbas, Shugaba Tinubu, yana da matukar son ganin Najeriya a yanayin da za ta iya amfani da damarmakin da za a samu ta hanyar aiwatar da yarjejeniyar ciniki cikin ’yanci a nahiyar Afirka.
“Hukumar Tattalin Arziki ta Majalisar Dinkin Duniya na hasashen a zuwa shekarar 2050 da kasuwanci a nahiyar zai haura Dala tiriliyan 29,” in ji hadimin shugaban kasar.