Shugabanin kungiyar kasashe mambobin ECOWAS, za su gudanar da wani taron gaggawa ranar Lahadi a game da juyin mulkin da sojoji suka yi a Nijar.
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu wanda shi ne sabon Shugaban ECOWAS, zai jagoranci zaman wanda za a gudanar a Abuja, babban birnin Najeriya.
- ‘Mutum miliyan 20 na fama da ciwon hanta a Najeriya’
- Yau take ranar cika-ciki da cin jela a Kasar Hausa
Cikin wata sanarwa, Shugaba Tinubu ya yi Alla-wadai da juyin mulkin, inda kuma ya yi wa al’ummomin kasashen waje alkawarin cewa zai yi duk mai yiwuwa domin kare dimokuradiyya da kuma tabbatar da dorewar kyakkyawan shugabanci a yankin.
A kunshin sanarwa mai dauke da sa hannun Kakakin Fadar Shugaban Kasa, Dele Alake ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya sha alwashin kawo karshen matsalar juye-juyen mulki a Yammacin Afirka.
Shugaba Tinubu ya yi fatan wannan taron na su zai samar da matsaya guda wadda za ta ba da damar mayar da Jamhuriyar Nijar kan turbar dimokuradiyya.
Sanarwar ta kuma ci gaba da cewa Mataimakiyar Shugaban Amurka, Kamala Harris da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Gutters sun bukaci Bola Tinubu ya yi duk mai yiwuwa wajen dawo da martabar Jamhuriyar Nijar ta hanyar kwato ta daga hannun Sojoji a wata tattaunawa da su ta wayar tarho.