✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu zai halarci taron G20 a Indiya

Za a yi a taron G20 na wannan shekara a ranakun 9 da 10 ga watan Satumba a Indiya.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai halarci taron kasashen G20 da za a yi a birnin New Delhi na kasar Indiya a ranar 9 zuwa 10 ga watan Satumba.

Mai magana da yawunsa, Cif Ajuri Ngelale, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a yayin da yake yi wa manema labarai karin haske kan shirye-shiryen shugaban kasar gabanin taron.

A cewar Ngelale, Tinubu zai halarci taron ne domin jawo hankalin kasashen waje kai tsaye zuwa kasar tare da hada gwiwa masu zuba jari masu zaman kansu daga sassan duniya don bunkasa ababen more rayuwa a Najeriya.

Ya ce Tinubu zai gabatar da jawabai yayin taron, wanda ya hada da dukkan shugabannin kasashen da ke halarta da sauran manyan masana’antu da ‘yan kasuwa daga sassan duniya.

Mai magana da yawun shugaban kasar, ya ce shugaban zai gana da takwaransa na Brazil Lula da Silva da Silva, da shugaban gwamnatin Jamus, Olaf Schultz, da Firaministan Indiya, Narendra Modi, da Shugaban Koriya ta Kudu, Yoon Suk Yeol, da wasu wasu tsirarun shugabannin kasashe kan batun taron G20.

Ana iya tuna cewa, tun a watan Yulin da ya gabata ne Gwamnatin Indiya ta gayyaci shugaba Bola Ahmed Tinubu zuwa taron na kasashen G20.

Taron ana yin shi duk shekara wanda aka fara tun lokacin da aka kafa shi a shekarar 2008 bayan rikicin kudi na duniya na 1997-1998.

Taron na G20 ya tattaro manyan kasashe masu muhimmancin tattalin arziki na duniya tare da mambobin da ke wakiltar kashi 75 na cinikayyar kasa da kasa da kashi biyu bisa uku na al’ummar duniya.

Da yake magana tun a watan Yuli kan shirin samun shugaba Tinubu ya halarci taron, Babban Jakadan Indiya a Najeriya, Ambasada Shri G. Balasubramanian, ya ce an riga an bude hanyoyin sadarwa tsakanin kasashen biyu don halartar Shugaba Tinubu.

“Don haka dangane da haka, muna sa ran mai girma Mista Bola Tinubu, shugaban kasar Najeriya zai ziyarci kasar Indiya domin taron G20 mai zuwa.

“Taron da za a yi a Indiya a ranakun 9 da 10 ga watan Satumba na wannan shekara,” inji shi.

“Don haka wannan wani abu ne da muke aiki kafada da kafada da hukumomin Najeriya.

“Mun yi tarurruka sama da 140 daga watan Disamba zuwa yanzu kuma mun gamsu sosai da halartar Najeriya a taron G20 da kuma a matakin ministoci, matakin kungiyar aiki, matakin rukuni, da dai sauransu.”

Mambobin G20 sun hada da: Argentina, Australia, Brazil, Canada, China, Faransa, Jamus, Indiya, Indonesia, Italiya, Japan, Jamhuriyar Koriya, Mexico, Rasha, Saudi Arabia, Afirka ta Kudu, Turkiyya, Birtaniya, Amurka, da Tarayyar Turai.