✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu zai halarci taron G20 a Brazil

Tinubu zai tafi Brazil ne, kwanaki kaɗan bayan dawowa daga ƙasar Saudiyya.

Shugaba Bola Tinubu zai tafi Brazil don halartar taron shugabannin ƙasashen duniya 20 (G20) na karo na 19, wanda zai gudana a birnin Rio de Janeiro, na ƙasar Brazil.

Taron ƙasashen zai gudana ne a ranar 18 da 19 ga watan Nuwamba, 2024.

Tafiyar na zuwa ne bayan dawowarsa daga taron ƙasashen Larabawa da Musulunci da aka yi a ƙasar Saudiyya.

Mai bai wa shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya sanar da hakan cikin wata sanarwa a ranar Lahadi.

Ya ce, “Gayyatar Shugaban Najeriya ya biyo bayan kiran Shugaban Brazil, Luiz Inacio Lula da Silva, wanda shi ne Shugaban G20 na yanzu.

“Taron zai tattauna batutuwan duniya kamar yaƙi da yunwa da talauci, sauyi a ɓangaren makamashi, da gyaran harkokin mulkin duniya.”

Jigon taron shi ne “Gina Duniya Mai Adalci da Ɗorewa.”

Ana kuma sa ran Tinubu zai tattauna da shugabanni ƙasashe daban-daban domin bunƙasa tattalin arziƙin Najeriya.

Zai samu rakiyar wasu manyan jami’an gwamnati, ciki har da Ministocin Harkokin Waje da na Noma.

Onanuga ya ƙara da cewa, “Shugaban zai dawo Najeriya da zarar an kammala taron.”