✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tinubu ya ziyarci Obasanjo kan takararsa ta shugaban kasa

A karon farko Tinubu ya kai wa Obasanjo ziyarar girmamawa kan takararsa ta 2023

A ranar Laraba dan takarar shugaban kasa a Jam’iyar APC, Bola Tinubu, ya kai wa tsohon Shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, ziyarar girmamawa kan takararsa ta 2023.

Sakataren yada labaran Gwamna Dapo Abiodun na Jihar Ogun, Kunle Somorin, ya sanar cewa a yayin ziyarar, Tinubu zai yi wa jama’a jawabi, bayan ya ziyarci Obasanjo.

“Zai ziyarci Obasanjo, daga nan ya gana da mutane a filin wasa na MKO Abiola,” inji sanarwar.

Shugaban Jam’iyyar APC a jihar, Yemi Sanusi, ya yi kira ga jagorarin jam’iyyar da su tabbatar sun fito tarbar dan takarar.

Wannan dai shi ne karon na farko da Tinuba ya ziyarci Obasanjon, ko da yake ba ita ba ce ziyararsa ta farko zuwa jihar.

A baya dai Tinubun da Obasanjon ba sa ga maciji, musamman lokacin da Obasanjon ke shugaban kasa, shi kuma yake Gwamnan Jihar Legas.

Sai dai a shekarar 2013, Tinubu ya yi watsi da adwarsu, inda ya roki Obasanjon da ya nuna musu dan takarar da ya fi cancanta ya shugabanci Najeriya a 2015, a matsayinsa na wanda ya tsallake siradin kabilanci ya shugabance ta a baya har sau biyu.

To sai dai nasarar Shugaba Buhari a zaben 2015 ya sauya akalar siyasar Tinubun, inda ya koma bayansa.

A hannu guda kuma Obasanjon a baya-bayan nan ya yi alkawarin kin nuna goyon baya ga kowanne dan takara a bayyane a zaben mai zuwa.