✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya ziyarci Buhari a Daura

Tinubu ya kai wa Buhari ziyarar ne bayan lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar Asabar.

Zababben Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari a mahaifarsa ta Daura da ke Jihar Katsina.

Tinubu ya sauka a filin jirgin sama na Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina tare da Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu da sauran jiga-jigan jam’iyyar a Yammacin wannan Larabar.

Gwamna Aminu Bello Masari na Jihar Katsina da mataimakinsa, Mannir Yakubu da sauran jami’an gwamnati ne suka tarbi tawagar Tinubu da ta kama hanyar zuwa Daura.

Bayanai sun ce Masari ya shiga cikin tawagar tawagar da ta kai ziyara Daura domin gabatar wa Shugaba Buhari Zababben Shugaban Kasar.

Tinubu dai ya yi nasara a kan sauran abokan takararsa da kuri’u 8,794,726.

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa kuma dan takara a babbar jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar ne ya zo na biyu da kuri’a 6,984,520.

Dan takarar Jam’iyyar LP, Peter Obi, tsohon Gwamnan Jihar Anambra ya zo a matsayi na uku da kuri’a 6,101,533 a yayin da tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma dan takarar jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya samu kuri’a 1,496,687 a matsayin na hudu.

Tun kafin a kai ga sanar da sakamakon zaben na karshe dai jam’iyyun PDP da LP da wasu suka yi fatali da shi, bisa zargin magudi da saba Dokar Zabe, inda suka ce za su shigar da kara a gaban kotu.

Sai dai kuma daga cikin jam’iyyu 18 da ake da su a Najeriya, 11 sun nesanta kansu da boren da PDP ta jagoranta na ficewa daga Cibiyar Tattara Sakamakon Zaben Shugaban Kasar da ya gudana a Abuja.

Farfesa Mahmood Yububu ya bayyana cewa ’yan Najeriya 93,469,008 ne ke da katin zabe kuma an tantance 25,286,616 daga cikinsu a zaben na ranar Asabar.

Daga cikin adadin, mutum 24,965,218 ne suka kada kuri’a, inda aka samu sahihan kuri’u 24,025,940 da kuma guda 939,278 da suka lalace.