Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bi sahun shugabannin duniya wajen aike da saƙon jaje ga tsohon shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump da aka kai wa hari a ranar Asabar.
Shugabannin ƙasashen duniya na ci gaba da mayar da martani da kuma miƙa saƙon jajen su ga ɗan takarar jam’iyyar Republican.
- Sojoji Sun Kashe ’Yan Ta’adda 3, Sun Ceto Mutum 22 A Borno
- A daina kallon fina-finan Hausa na zamani — Jami’ar Danfodiyo
A sanarwar da mai magana da yawun Tinubu ya fitar, Ajuri Ngelale, ya ce “harin da aka kai wa tsohon shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, abun ƙyama ne kuma ya wuce ƙololuwar ƙa’idojin dimokuraɗiyya.
“Ina miƙa jajena ga tsohon shugaban ƙasar tare da fatan samun sauƙi.
“Ina kuma jajanta wa iyalan waɗanda suka rasu da waɗanda suka jikkata da fatan Allah Ya basu lafiya.
“Najeriya na tare da Amurka a wannan lokaci” in ji Tinubu.
Aminiya ta ruwaito yadda aka harbi tsohon shugaban na Amurka, yayin da yake tsaka da jawabi a wani taron yaƙin neman zaɓe a Jihar Pennsylvania.
Nan da nan dai jami’an leƙen asirin suka yi wa tsohon shugaban ƙasar rumfa tare da lulluɓe shi a yayin da suka kai masa ɗauki.
Bidiyon lamarin ya karaɗe dandalin sada zumunta na X, ya nuna yadda tsohon shugaban ƙasar ya yi gaggawar sunkuyawa tare da riƙe ɓarin kunnensa na dama inda aka harba yana kwararar da jini.