✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaba Tinubu ya yi alhinin rasuwar Sheikh Abubakar Giro Argungu

Tinubu ya bayyana rasuwar malamin a matsayin babban rashi ga kasar baki daya

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya mika sakon ta’aziyarsa zuwa ga iyalai, ’yan uwa da abokan arziki da kuma daliban fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Abubakar Giro Argungu wanda ya rasu a ranar Laraba da daddare.

Shugaban Kasar ya bayyana rasuwar malamin a matsayin babban rashi ga kasar baki daya, ba ga dalibansa kadai ba, duba da yadda malamin ya dade yana bayar da gudunmuwa wajen wa’azi da gyaran tarbiya.

 

“Za a dade ba a manta Sheikh Giro ba saboda yadda aka dade ana jin muryarsa wajen karatuttuka, wa’azi da sauran hanyoyin gyara tarbiya.

“Kokarin malamin ya dade yana yi karkashin Kungiyar Izala, wadda ya taba jagoranta, ya yi tasiri kwarai wajen wa’azantarwa da shiryar da matasan Musulmi hanya madaidaiciya,” inji shi ta bakin Ajuri Ngelale, Mashawarcin Shugaban Kasa shawara na musamman kan harkokin yadda labarai.

Shugaban Kasar ya kara da cewa za a yi kewar Sheikh Giro musamman a matsayin malama mara tsoro wajen aikawa da sakonsa da kuma jawo hankalin gwamnati wajen sauke nauyin da Allah Ya dora musu na yi wa al’umma aiki.

Ya kuma mika ta’aziyarsa da jaje ga Gwamnatin Jihar Kebbi da mutanenta da Musulman Najeriya baki daya bisa wannan babban rashi, sannan ya yi addu’ar Allah Ya jikan malamin.