Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi ta’aziyar mutuwar fitaccen ɗan wasan kwaikwayo Usman Baba Pategi wanda aka fi sani da ‘Samanja Mazan Fama’.
Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Ajuri Ngelale ya fitar, ya ce Shugaban ya kwatanta mutuwar da abu mai ciwo, inda ya ce Samanja ya ba da gudummawa a ƙasar ta hanyoyi daban-daban a tsawon rayuwarsa.
- Yadda muka tsinci kanmu a ranar farko ta yajin aikin NLC — Kanawa
- Jerin ’yan Super Eagles 23 da za su buga wasannin neman shiga Gasar Kofin Duniya
Ya ce faɗakarwa da marigayin ya riƙa yi ta hanyar wasannin kwaikwayo, sun koyar da matasan ƙasar da dama abubuwa masu kyau.
Shugaba Tinubu ya buƙaci iyalan Pategi, da al’ummar jihohin Neja da Kwara, da masarautar Pategi, da masana’antar harkar nishaɗi da su ɗauki dangana.
Ya rasu ne a daren Asabar bayan fama da jinya mai tsawo, inda ya bar mata biyu da ’ya’ya 12.
Mohamm Samanja, wanda tsohon soja ne, daga baya ya zama ma’aikacin Gidan Rediyon Tarayya na Kaduna, ya yi fice a matsayin shahararren dan wasan kwaikwayo da suna Samanja Mazan Fama.