Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ya aiwatar da wasu sauye-sauye a majalisar ministocinsa da ya rabawa ma’aikatu a makon jiya.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai bai wa Shugaban Kasar Shawara ta Musamman kan Harkokin Yada Labarai, Ajuri Ngelale ya fitar a Yammacin wannan Lahadin.
- NDLEA ta kama dalar Amurka miliyan 20 ta jabu a Abuja
- Ba za mu yarda sojoji su mulki Nijar tsawon shekara uku ba — ECOWAS
A sauye-sauyen, Tinubu ya dauke Injiniya Abubakar Momoh daga Ma’aikatar Matasa zuwa Ma’aikatar Harkokin Neja Delta.
Ajuri Ngelale ya ce nan gaba kadan za a sanar da ministan da zai a dankawa akalar jagorancin Ma’aikatar Matasan.
Sanarwar ta ce Tinubu ya ba da umarnin aiwatar da sauye-sauye a ma’aikatun Sufuri, Harkokin Cikin Gida da kuma Tattalin Arziki na Ruwa.
Ministocin da lamarin ya shafa sun hada da Adegboyega Oyetola wanda a yanzu aka mayar da shi Ministan Tattalin Arziki na Ruwa
Haka kuma, an mayar da Bunmi Tunji-Ojo zuwa Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida yayin da Sa’idu Alkali ya koma Ma’aikatar Sufuri.
Kazalika, sanarwar ta ce Kananan Ministocin man fetur da iskar gas za su kasance a karkashin ma’aikata daya, wato Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur.
Ministocin su ne; Heineken Lokpobiri a matsayin Karamin Ministan Man Fetur. Sai kuma Ekperipe Ekpo a matsayin Karamin Ministan Gas.
Haka kuma, Shugaba Tinubu ya amince da sauya sunan Ma’aikatar Kula da Muhalli da Rayuwar Halittu a matsayin Ma’aikatar Muhalli.