Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya taya John Dramani Mahama murnar lashe zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a Ghana a ranar 7 ga watan Disamba, 2024.
A wata hira ta wayar tarho, Tinubu ya yi fatan wa’adin Mahama na biyu zai ƙara kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Yammacin Afirka, musamman a matsayinsa na shugaban ECOWAS.
- ’Yan bindiga sun sace amarya da ƙwayenta 4 a Sakkwato
- Yadda jadawalin FIFA Club World Cup na bana ya kasance
Tinubu, ya yaba wa ’yan Ghana bisa gudanar da zaɓe cikin kwanciyar hankali, inda ya bayyana cewa wannan alama ce ta jajircewarsu ga dimokuraɗiyya.
Haka kuma, ya jinjina wa ɗan takarar jam’iyyar mai mulki, Dokta Mahamudu Bawumia, bisa karɓar faɗuwa kafin sanar da sakamakon zaɓen, abin da ya ƙara ƙarfafa dimokuraɗiyyar ƙasar Ghana.
Tinubu, ya bayyana cewa dawowar Mahama matsayin shugaban ƙasa ya nuna yadda ’yan Ghana suka yi amana da jagorancinsa.
Ya kuma tabbatar da aniyar Najeriya na ƙara danƙon zumunci da Ghana tare da gode wa shugaban ƙasa mai barin gado, Nana Akufo-Addo, bisa irin gudummawar da ya bayar wajen ci gaban ƙasar da zaman lafiya a yankin.
Shugaba Tinubu ya ce yana sa ran yin aiki tare da Mahama domin ƙarfafa haɗin kai da ci gaba a yankin Yammacin Afirka.