Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya umarci Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Najeriya (FAAN) ta canza wa wasu filaye 15 zuwa sunan wasu fitattun ’yan Najeriya.
Daga cikin sunayen har da filin jirgin sama na Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, wanda aka saka wa sunan tsohon Shuagaban Kasa, Muhammadu Buhari.
- Shugaban NUC ya ajiye mukaminsa, zai koma koyarwa a BUK
- Hajjin bana: Tukari sun mamaye masaukan alhazan Najeriya a Mina
Umarnin dai na kunshe a cikin wata wasika da aka aike wa dukkan Shugabannin Gudanarwa na filayen jiragen, wacce ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama ta aike mai dauke da kwanan watan 1 ga watan Yunin 2023.
Wasikar na dauke ne da sa hannun Daraktar Kula da Filayen a Ma’aikatar, Misis Joke Olatunji.
Ga cikakkun filayen da sunayen wadanda aka sanya musu
- Filin jirgin sama na Akure – Olumuyiwa Bernard Aliu
- Filin jirgin sama na Benin – Oba Akenzua II
- Filin jirgin sama naDutse – Muhammad Nuhu Sanusi
- Filin jirgin sama naEbonyi – Chuba Okadigbo
- Filin jirgin sama naGombe – Birgediya Zakari Maimalari
- Filin jirgin sama naIbadan – Samuel Ladoke Akintola
- Filin jirgin sama naIlorin – Janar Tunde Idiagbon
- Filin jirgin sama naKaduna – Hassan Usman Katsina
- Filin jirgin sama naMaiduguri – Janar Mumammadu Buhari
- Filin jirgin sama naMakurdi – Joseph Sarwuan Tarka
- Filin jirgin sama naMinna – Mallam Abubakar Imam
- Filin jirgin sama naNassarawa – Sheikh Usmanu Dan Fodio
- Filin jirgin sama naOsubi – Alfred Diete Spiff
- Filin jirgin sama naFatakwal – Obafemi Awolowo
- Filin jirgin sama naYola – Lamido Aliyu Mustapha